HUKUNCIN AUREN KISAN WUTA


AMBAYA TA 153
******************
Assalamu alaikum
Minene hukuncin Auren Dibar wuta a Musulunci?

Shin hukuncin Yana da bambanci idan Macce ce ta shirya Auren Dibar wutar ba tareda
sanin tsohon Mijinta ba?

Minene hukuncin idan matar da Mijin suka shirya Auren Dibar wutar?

Sannan hukuncin
yana da bambanci idan sabon mijin da Aka Aura yana da Masaniya akan Auren Dibar wuta ne za ayi dashi?

(daga Barrister Isma'il)

AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatulLah.

Wannan tambayar mun riga mun amsa irinta achan baya. Amma saboda muhimmancin Mas'alar, da kuma yawan faruwarka acikin al'ummah, sai naga cewa ya zama wajibi mu sake amsa wannan dinma.

Imamuz-Zahabiy (rah) ya fada acikin shahararren littafinsa mai suna "KITABUL-KABA'IR" akan shafi na 141, Laifi na 53, yana cewa:

Hadisi ya inganta daga Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (ra) yana cewa: "MANZON ALLAH ﷺ YA TSINEWA MAI AUREN KISAN WUTA, DA KUMA WANDA AKAYI AUREN KISAN WUTAN DOMINSA".

Imam Tirmidhy (rah) yace:
Aiki abisa wannan fahimtar (rashin halarcin auren kisan wuta ta kowacce fuska) ya tabbata agun ma'abota ilimi. Daga cikinsu akwai

Umar bn Khattab,
Uthman bn Affan
Abdullahi bn Umar (Allah shi Qara yarda dasu).

kuma wannan shine fahimtar FUQAHA'U daga tabi'ai.

Imamu Ahmad bn Hanbal da Imamun Nisa'iy su ma sun ruwaito irin wannan hadisin Da isnadai masu inganci.

Wani mutum ya tambayi Abdullahi bn Umar (ra) cewar:

"YAYA KAKE GANI? Shin ya halatta in auri matar da wani mutum ya saki domin in halatta ta agareshi??

Sai ya amsa masa da cewar:

A'a bai halatta ba.  sai dai in zaka aureta, to ka aureta domin kwadayin zama da ita, idan kaga tayi maka shikenan ka zauna da ita.. Idan kuma bata yi maka ba ka saketa. (Amma auren kisan wuta haramun ne). Ya ci gaba da cewa: MUN KASANCE MUNA QIRGA SHI (irin wannan auren) AMATSAYIN KWARTANCI AZAMANIN MANZON ALLAH ﷺ.

Imamul-Athram da Ibnul-Munzir sun daga Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) yana cewa:

"BA'A TA'BA ZUWA MIN DA MASU AUREN KISAN WUTA BA, FACHE SAI NA JEFESU (RAJAMUWATO JIFA IRIN NA HADDI).

Wani Mutum ya saki matarsa (Saki uku) dama kuma 'Yar baffansa ce, Sai daga baya ya dawo yana nadama, sai wani mutum kuma yazo yake tambayar Sayyiduna Abdullahi bn Umar (radhiyalLahu anhu) cewa: Shin ya halatta inje in aureta, (daga baya in saketa) domin in halasta masa ita??"

Sai yace masa "Zaman Zina sukeyi koda sun kai shekara 20 suna tare. In dai an daura auren da wannan niyyar.

Imam Ibrahim An-Nakha'iy yace IN DAI DAYAN CIKIN MUTUM UKUN NAN (wato mijin farko, ko miji na biyu, ko kuma ita matar) INDAI WANI DAGA CIKINSU YAYI NUFIN AUREN KISAN WUTA, TO AUREN NA BIYUN DANA FARKON DUK SUN LALACE. (Dama bai halatta ba). KUMA DUK DA HAKA MATAR BA TA HALATTU GA WANCAN MIJINTA NA FARI BA (Koda ta dawo hannunsa).

Imam Hasanul-Basary ma yace: In dai dayan cikin mutum ukun nan yayi niyyar auren kisan wutan, to auren ya 'baci.

Daga Cikin wadanda suke kan wannan fahimtar akwai:

IMAMU MALIK
SUFYANUTH THAURY
IMAMU AHMAD BN HANBAL
IMAM LAYTHU BN SA'AD.

Irin wannan auren bai halatta ma tun farko adaura shi ba (Mutukar Malamai da waliyyan auren sun fahimci niyyar masu auren)  Kuma ya kamata hukuma ta rika ladabtar da dukkan wadanda aka samesu da hannu aciki.

WALLAHU A'ALAM.,

DAGA ZAUREN FIQHU JUNE 15 2013 (ANYI RUBUTUN NAN TUN SHEKARU 12 DA SUKA GABATA). YA ALLAH KA SANYA IKHLASI CIKIN DUKKAN AYYUKANMU AMEEN.
EMAIL ADDRESS : zaurenfiqhu@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI

MAGANIN KAIKAYIN GABA