MU SAN ANNABINMU (19)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Salatai da amincin Allah Madaukaki su tabbata ga Fiyayyen Annabawansa, Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da mabiyansa da mataimakansa har zuwa ranar sakamako.
Wannan shine kashi na goma sha tara (19) acikin darasin tarihin Manzon Allah (saww) wanda ke zuwa muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp.
ISRA'I DA MI'IRAJI
******************
Shin menene ma'anar kalmar ISRA'I? : Ma'anarsa ita ce duk wata tafiya da aka yita acikin dare. Shi kuwa Mi'iraji ma'anarsa shine tafiya zuwa sama.
Kuma wannan muhimmin al'amari ya faru ne agarin Makkah, kafin hijirah zuwa Madeena da shekara guda da rabi.
Watarana sai ga Mala'ika Jibreelu yazo wajen Manzon Allah (saww) acikin dare tare da Buraqah. Wata dabba ce wacce keda jiki irin na doki kuma tana da kai irin na mutane, sannan tana da fukafukai ajikinta tana da tsananin saurin tafiya amma babu mai hawanta sai Annabawa alaihimus salam.
Dabbar tana magana kamar yadda Dan Adam ke yi, Kuma tana ajiye Qafarta ne a Karshen wajen da idanuwanta suka hanga.
Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya hau bayanta suka tafi zuwa Masallacin Qudus inda ya tarar da dukkan Annabawa (alaihimus salam) sun taru sukayi masa maraba, sannan ya wuce yayi musu Limancin sallah. Wanda yin hakan yana nuni ne zuwa ga fifikon darajarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Daga nan sai suka tafi zuwa sama ta-daya tare da Mala'ika Jibreelu (alaihis salam) inda suka iske Annabi Adam (alaihis salam) yayi masa maraba, yayi masa kirari yana cewa "Madalla da 'Da nagari, Annabi mai nasiha" (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Kuma acikin wata riwayar ya tarar da Mala'ikun dake wajen sunyi sahu-sahu, ya wuce yayi musu sallah bisa Addinin Kakansa Annabi Ibraheem (alaihis salam).
Daga nan suka wuce zuwa sama ta biyu inda ya tarar da Annabi Isa da Annabi Yahya (alaihimas salam). Sunyi masa maraba tare da gaisuwa suna cewa "Madalla da 'dan uwa nagari, Annabi mai nasiha (saww)". Anan dinma yayi wa Mala'iku sallah sannan suka wuce sama ta-uku.
Anan ne ya hadu da Annabi Yusufu 'dan Annabi Ya'aqub (alaihimas salam) wanda shi aka ba wa rabin kyawu. Yayi maraba dashi tare da gaisuwa ta girmamawa sannan suka wuce zuwa sama ta-hudu.
Anan sama ta-hudu din ne ya hadu da 'daya daga cikin Kakannin Annabawa (as) wato Annabi Idrees (alaihis salam) wanda shi dama tun farko anan aka karbi ransa, kuma anan yake zaune. Yayi maraba dashi kuma ya gaisheshi sannan suka tafi zuwa sama ta-biyar.
Anan sama ta-biyar din ne suka hadu da Annabi Haruna (alaihis salam) shima yayi maraba dashi tare da gaisuwar girmamawa. Daga nan suka wuce zuwa sama ta shida inda suka hadu da Annabi Musa 'dan Imrana (alaihis salam) shima ya gaisheshi ya girmamashi.
Daga nan suka wuce zuwa sama ta-bakwai inda yaga wani Masallaci da ake kira Baitul Ma'amur. Shi wannan masallacin yana daidai kan saitin dakin ka'abah ne. Kuma Mala'iku dubu saba'in ne suke ziyartarsa a kowacce rana. To ajikinsa ne yaga Kakansa Annabi Ibraheem (alaihis salam) yana zaune akan kujerar haske, ya jingina bayansa da jikin dakin.
Ya mike tsaye ya gaisheshi yayi farin ciki dashi yace masa "Madalla da 'Da nagari, Annabi Mai nasiha".
Daga nan suka wuce zuwa "SIDRATUL MUNTAHA" (Wato magaryar tikewa) wata bishiya ce wacce lamarin buwayar Ubangiji ke lullube da ita. Daga nan ne Mala'ika Jibreelu ya tsaya. Sai Annabi (saww) yace masa "Ya Jibreelu shin anan ne Masoyi ke rabuwa da masoyi?".
Sai yace "Ya Muhammadu nan ne iyakar matsayina. Kai idan ka Qara gaba zaka wuce, amma ni idan nayi gaba Qonewa zanyi". (ALLAHU AKBAR).
Daga nan bayan ya keta hijabai na haske sai ya isa zuwa wani waje wanda babu wani Mahalukin da ya ta'ba zuwa. Anan ne Ubangijinsa mai girma da buwaya ya gana dashi, yayi zance dashi, yayi masa baiwa dashi da al'ummarsa, sannan ya farlanta masa salloli guda hamsin dashi da al'ummarsa. Ya nemi rangwame har aka dawo dasu salloli biyar bisa shawarar da Annabi Musa (as) ya rika bashi.
Yayin da Annabi (saww) ya dawo garin Makkah, bayan gari ya waye ya basu labarin abinda ya faru dashi acikin dare, sai masu Qarfin imani suka gaskatashi. Masu raunin imani kuma sukayi riddah. Su kuwa kafirai suna bisa kafircinsu.
Ya Allah ka Qara salati da aminci da girma da mutunci da alfarma bisa wannan Annabi mai girma tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da mabiyansa har zuwa ranar rarrabewa.
An gabatar da wannan karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp 4 ranar 09/03/2019 03/07/1440.
Comments
Post a Comment