DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) - 1
DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) 1
*************************************
Yana daga cikin Khasa'isu na Annabi Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa Allah ya sanya soyayyarsa azukatan halittu masu motsi har ma marassa motsi.
Mun kawo muku Qissar duwatsun dake yin gaisuwa gareshi tun tasowarsa agarin Makkah. Kuma mun gaya muku labarin wani dutsen dake gaisheshi bayan an fara yi masa wahayi. Sannan mun gaya muku Qissar da aka ruwaito daga Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (rta) game da duwatsu da bishiyoyin dake yin gaisuwa ga Manzon Allah (saww).
Daga cikin duwatsun duniya wadanda soyayyarsu ga Manzon Allah (saww) ta bayyana Qarara afili, dutsen Uhudu yana kan gaba..
Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace "Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya hau kan Dutsen Uhudu tare da Abubakar da Umar da Uthman (Radhiyallahu anhum). Sai dutsen yayi girgiza dasu (Saboda Shauqin jin tafin Qafar Manzon Allah akansa).
Sai Manzon Allah (saww) ya bugeshi da Qafarsa mai daraja, Sannan yace masa "NUTSU YA UHUDU! DOMIN KUWA ANNABI NE ABAYANKA DA SIDDEEIQI DA KUMA SHAHIDAI GUDA BIYU".
(Imamul Bukhariy ne ya ruwaitoshi).
Uhudu dutse ne a gefen garin Madeenah. Kuma shine wanda Manzon Allah (saww) yayi masa Kyakkyawar shaidar Soyayya wacce koda acikin Sahabbai ba kowa ne ya sameta ba.
Annabi (saww) yace :
"UHUDU DUTSE NE DAKE SONMU, MUMA MUNA SONSA".
(Imamul Bukhariy ne ya ruwaitoshi).
Salati da amincin Allah adadin numfashi da motsin dukkan halittu ya tabbata acikin kowacce Qiftawar ido bisa Annabinmu Shugabanmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa Yardaddu da dukkan Salihan bayin Allah har zuwa ranar sakamako. Da albarkar wannan salatin ya Allah ka gafarta ma Mahaifanmu da Malumanmu da dukkan marigayanmu, ka kyautata karshenmu kasa mu cika da imani cikin Tsananin bege da Shauqi ga Annabinka (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (05-11-2017 16-02-1439).
Comments
Post a Comment