FA'IDODIN TSAMIYA DAGA ZAUREN FIQHU
Tsamiya wata bishiya ce wacce ake shukata kuma ana magani da ita tun kusan shekaru dubu uku da suka gaba. Kuma ana samunta acikin dazuzzukan nahiyarmu ta Afirka da kuma kudancin nahiyar Asia.
Likitocin Musulunci sun dade suna amfani da 'ya'yan bishiyar domin magance larurori masu yawa, haka kuma ana amfani da ita wajen hada nau'o'in abinci da abinsha.
'Ya'yan wannan bishiya ta tsamiya suna kunshe da sinadarai masu yawa sosai wadanda ke Qara ma jikin Dan Adam amfani mai yawa. Misali :
- Vitamin A 151, Vitamin E, Vitamin B da kuma C. Sannan acikinta akwai Calcium, Potassium, thiamine, Tartaric Acid, Phosphorous, Proteins, Magnesium, Riboflavin. Haka kuma sabobbin ganyenta suna kunshe da sinadarin Sulfur da Calcium mai yawan gaske.
Yanzu ga wasu fa'idodi ka'dan daga cikin dimbin abubuwan amfani dake cikin tsamiya :
1. CIWON ZUCIYA : Shan kunun tsamiya ko farau-farau (Juice) wanda aka yishi da tsamiya zai iya zama riga-kafi daga kamuwa da chutar hawan jini ko ciwon zuciya saboda sinadarin Calcium din dake cikinta yana taimaka wa jikin Dan Adam wajen sarrafa jini acikin jiki.
Sannan tsamiya tana taimaka wa wajen samun waraka daga chutar hawan jini saboda sinadarin dake cikinta yana taimakawa wajen zubar da mummunan sinadarin nan na Cholesterol wanda ke chutar da jiki.
Kuma tsamiya tana sanya hanyoyin jini su Qara taushi, kuma tana tsinka daskararren kitsen dake cikin bututun jinin dake jikin zuciya (Arteries).
2. CIWON SUGAR (DIABATES) : Acikin tsamiya akwai wani sinadari mai suna "ALPHA-AMYLASE" wanda yakan taimaka wa jikin dan Adam wajen narkar da Carbonhydrate wanda shine yake zama Sugar acikin jikin dan Adam.
Kuma yana taimaka wa hantar Dan Adam wajen daidaita yanayin Sugar wanda ke shiga cikin jinin Dan Adam.
3. MAGANIN ZAFIN JIKI : A samu garin Kamoon (wani tsiro ne ana samun shi a manyan Islamic chemist) a zubashi kamar cokali guda acikin kunun tsamiya arika sha. Yana magance daukar zafin da jikin mutum ke yi. Kuma yana taimaka wa jiki wajen fitar da chutuka ta cikin zufa.
4. GARKUWAR JIKI : Kasancewar akwai sinadarin "Vitamin C" mai yawa acikinta, tare da sauran sinadarai masu kashe kwayoyin chuta, tsamiya tana taimakawa wajen bunkasa Qarfin garkuwar jikin Dan Adam.
Kuma yana kashe kwayoyin chuta "Viruses, Parasites da sauransu tana hanasu sakewa acikin jini da gngar jikin Dan Adam.
5. RAGE QIBA : Tsamiya tana kunshe da wani sinadari wanda ke hana jikin Dan Adam yin ajiyar kitse. Don haka yawaitar shan juice din tsamiya ko kununta zai taimaka wa masu yunkurin rage Qiba in shaAllah.
Anan zamu tsaya amma in shaAllah acikin kashi na biyu zamu Qarasa kawo muku wasu fa'idodinta tare da kawo hanyoyin sarrafata.
An gabatar da darasin nan a Zauren Fiqhu Whatsapp ranar 01/04/2019 07064212990 (25/07/1440)
Mashah Allahu
ReplyDelete