SHIN KA TA'BA ZUBDA HAWAYE DOMINSA KUWA?
An zageshi, an Jefeshi da duwatsu, Anyi masa jina-Jina Sahabbansa sun nemi yayi addu'a a hallakar da duniyar amma yace A'a. Maimakon haka ma sai addu'ar alkhairi yayi ma mutanensa.
A lokacin da yaje ganawa da Ubangijinsa bai manta dani, da kai, da dukkan al'ummarsa ba. Sai da ya roka mana alkhairai masu yawa awajen Allah.
Yayi Hijira daga Makkah zuwa Madeena. Sun biyoshi domin su kasheshi amma duk da haka bai yi musu mummunar addu'a ba..
Ya jure yunwa da Kishirwa da Zafi da sanyi duk domin al'ummarsa su samu shiriya.
Aranar yakin Uhudu kafirai sunji masa rauni, amma duk da haka bai yi mummunar addu'a akansu ba. Saboda tausayi da Jin Qai irin nasa.
Mutanen garin Ta'if sunyi masa wauta wacce ba'a ta'ba yin kamarta ba. Amma duk da haka bai Tsine musu ba, kuma bai yi mummunar addu'a akansu ba.
Hakanan alokacin da zai bar duniya, Sai da ya tambayi Mala'ika Jibreelu ya gaya masa Alkawarurrukan da Ubangiji yayi ma al'ummarsa sannan ya samu kwanciyar hankali. Amma har ya bar duniya bai dena ambaton al'ummarsa ba.
Yana da wata addu'a ta Musamman wacce ya boyeta, ya tanadeta sai aranar Alqiyamah zai yi amfani da ita domin ceton Ma'abota Zunubi daga cikin al'ummarsa.
Ya Allah ka saka masa da mafificin sakamakofl fiye da irin wanda kake yiwa Annabawa da Manzanni akan al'ummarsu.
Ya Allah ka tabbatar masa da matsayin nan nasa na MAQAMUL MAHMOUD, Kuma ka sanyamu acikin na hannun damansa awannan ranar.
Salati da aminci su tabbata agareshi da iyalan gidansa gwargwadon Girman darajarsa awajenka Ya Allah..
WANNAN HADIYYAH CE DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP ZUWA GA ZUKATAN DUKKAN MASOYAN RASULULLAHI (SAWW).
Comments
Post a Comment