QISSAR YAQIN BADAR KASHI NA TARA

AN FARA GWABZAWA TSAKANIN JARUMAI

Acikin kashi na takwas mun tsaya ne adaidai wajen da Kowanne bangare sukayi sahu sahu, kuma Manzon Allah (saww) yayi addu'a yana cewa:

"Ya Allah Ga Quraishawa nan sun tunkaro da Alfaharinsu, suna jayayya da kai, kuma suna Qaryata Manzonka.. Ya Allah taimakon nan naka wanda kayi min alkawari".

Adaidai wannan lokacin sai wani sabani ya faru atsakanin manyan Askarawan Mushrikan Makkah.

Yayin da shi Utbatu bn Rabee'ah yake kokarin hana yin Yakin, yake kokarin kawai zai dauki fansa bisa dan uwan alkawarinsa wato Amru bn Alhadhramiy wanda Muminai suka kashe bisa kuskure, alokacin da suka fita wani Samame karkarin Sayyiduna Abdullahi bn Jahash.

Har ya fara jan ra'ayin sauran mutanensu akan haka, da Abu Jahal ya samu labari sai yace masa "Kai dai Rago ne. Amma mu kan wallahi ba zamu koma gida ba, har sai Allah yayi hukunci tsakaninmu da Muhammadu".

Ana cikin haka, Ashe su mushrikai Qishirwa ta fara cin addabarsu. Sai wani mai suna Al-Aswadu bn Abdil Asad Almakhzoumiy ya fito aguje, yace :

"NAYI MA ALLAH RANTSUWA, WALLAHI SAI NASHA RUWA DAGA RIJIYARSU, KO KUMA IN RUSHETA, KO KUMA IN BA HAKA BA SAI DAI IN MUTU KAFIN WAJEN".

Ya taho aguje sai Sayyiduna Hamzah ya fita ya tareshi ya sare masa sawayensa har wajen Kwabrinsa. Ya fadi rigingine, ya rika mirginawa har sai da ya tsunduma cikin rijiyar.

Yayi hakane don kubutar da rantsuwarsa wacce yayi. Amma Sayyiduna Hamzah ya bishi ya kasheshi kafin yasha ruwan.

Sai Manzon Allah (saww) ya mike ya fara yiwa Dakarun Musulunci WA'AZI yana jan hankulansu akan yin hakuri da juriya, kuma yana Qara kwadaitar dasu akan yin Jihadi.

Daga cikin abinda yake gaya musu, yana cewa : "HAKIKA SHI YIN JURIYA AWAJEN YAQI, YANA DAGA CIKIN ABINDA ALLAH YAKE TAFIYAR DA BAQIN CIKI DOMINSA, KUMA YANA TSERATARWA DAGA DAMUWA".

Daga nan sai aka fara yakin da salo irin na 'MUBARAZAH' wato fito na fito.

Mutum uku ne suka fara fitowa daga sahun Mushrikai. sune kamar haka:
1. UTBATU BN RABEE'AH.

2. SHAIBATU BN RABEE'AH.

3. WALEED BN UTBAH BN RABEE'AH.

Sai mutane uku daga Al-Ansar (Mutanen Madeenah) suka fita domin tararsu. Sai suka ce "Mu bamu da bukatarku. Mu Muna nufin daidai damu su fito daga 'Ya'yan Baffanin nan namu (Suna nufin wai daga 'ya'yan Abdul Muttalibi).

Sai Manzon Allah (saww) ya fitar musu da nasa mutanen guda uku kamar haka:

1. UBAIDAH BN ALHARITH BN ABDIL MUTTALIB (RA).

2. HAMZAH BN ABDIL MUTTALIB. (RA)

3. ALIYU BN ABI TALIB BN ABDIL MUTTALIB (RA)

Sai Sayyiduna Ubaidah ya tari Utbatu bn Rabee'ah. Shi kuma Hamzah ya tari Shaibatu bn Rabee'ah, shi kuma Sayyidi Aliy ya tari Waleedu bn Utbah..

An fara gwabzawa tsakanin Gwanayen yaki.. Jarumai sun fara fafatawa...

Kafin wani lokaci Sayyidi Hamzah ya kashe Shaibatu, ya aikashi Jahannama... Shima Sayyidi Ali ya kashe Waleedu (dama sa'ansa ne tun a Makkah. Kuma alokacin ma yayi sabon aure).

Kafin yakin yayi nisa Sayyidi Aliy ya sare masa hannu, sannan yayi masa kisa irin na Jaruman fama..

Shi kuwa Ubaidah, dashi da Utbatu sunyi ma juna rauni sosai amma babu wanda ya kashe wani. Sai da Sayyidi Aliy da Hamzah suka zo suka Qarasa kashewa kafirin wato Utbatu. Shi kuma Ubaidah aka daukeshi zuwa waje (bayan fage kenan). Aka kwantar dashi acikin rumfar da Annabi (saww) yake ciki.

Alokacin nan an sareshi a kafarsa har 'bargon Qafarsa yana tsiyaya.. Sai Annabi (saww) ya shimfida kafarsa mai daraja, Ubaidah ya tasa kai da ita... Ya dora kumatunsa akanta. Annabi (saww) yayi masa kyakkyawan albishir din samun mutuwar Shahada.

Shi kuma Ubaidah yana cewa "Naso ace Abu Talib yana da ransa, domin ya san cewa mune muka fi chanchanta da Qaulinsa (acikin wakar da yayi ma Manzon Allah saww) yana cewa:

"ZAMU KARESHI HAR SAI AN KASHEMU AGEFENSA, KUMA ZAMU MANCE DA 'YA'YANMU DA MATAYENMU (SABODA SHI).

Wadannan baitukan Abu Talib ne wadanda ya rera ma Manzon Allah (saww).

Anan zan tsaya sai a kashi na goma kuma.

Fatan ZAUREN FIQHU shine, Allah shi Qara mana Son MANZON ALLAH (saww) soyayyar da babu fatara bayanta. Ya Qara mana kusanci dashi, kusancin da babu nesanta bayansa.  Aaameeen thumma aaameeen.

An gudanar da karatun ne acikin ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI