ILLOLIN SHAN TABAR WEEWI

Acikin 'yan shekarun nan da matasa suka lalata kansu ta hanyar amfani da miyagun kwayoyi, Tabar Weewi ita ce kan gaba fiye da dukkan miyagun Kwayoyin da matasan suke amfani dasu.

Wannan yasa ZAUREN FIQHU ya gudanar da bincike akanta domin ganowa irin illolinta, da kuma yadda take aiki wajen ruguza lafiyar jikin masu ta'ammali da ita.

SUNAYENTA
*************
Kasancewar ana amfani da ita kusan adukkan nahiyoyin duniya, wannan yasa Tabar Weewi take da sunaye kala-kala kamar haka:

WEEWI, Ganye, Marijuana, Indian Hemp, Ganja, Pot, Igbo, Weed, Canabees, Hasheesh, Texas Tea, da dai sauransu.

ILLOLINTA
***********
Ganyen tabar WEEWI yana kunshe da Sinadarai sama da guda Arba'in masu chutar da lafiyar 'Dan Adam. Daga cikinsu har da sinadarin TETRA-HYDRO-CANNABINOL (T.H.C.) wani mummunan sinadari ne wanda yake chanza ma kwakwalwar 'Dan Adam yanayin yadda take karbar sakonni da yadda take sarrafa su.

Duk lokacin da mashayin Weewi ya Zuki hayakinta, shi wannan Mummunan sinadari yakan ratsa ta cikin hunhu (LUNGS) ya shiga ta cikin jini, ya zuba mummunan dafi acikinsa, sannan ya ratsa ya shiga dukkan Systems na jikin mutum.. Musamman ma Kwakwalwa da kuma Zuciyar 'Dan Adam.

Daga nan zai sanya zuciya ta riga bugawa da karfi fiye da yadda ya kamata ta rika yi. wannan yake haifar da Hawan jini da kuma ciwon zuciya ga mafiya yawan masu shanta.

Ga kwakwalwa kuma, sinadarin tabar Weewi yana mamayewa bangarorin kwakwalwa wadanda suke da alhakin sarrafa Tunani, da kuma karbar bayanan lissafi, da kuma dabi'ar 'Dan Adam.

Acikin Minti talatin (30 mins) na farkon lokacin da mashayin Weewi ya zuketa, zai jishi acikin wani yanayi kamar amafarki. wato zai ji tamkar mafarki yake yi, amma kuma gashi afarke. wannan ne yake haifar da kidimewa ga wadanda basu saba zukarta ba.

Qara ma kwakwalwa gudu da take yi, da kuma Qaruwar Karfi bugun zuciya shi yake haifar da wani yanayi ga nasu Zukarta, zasu jisu kamar asama suke...

Wasu sun dauka cewar Tabar Weewi tana Qara musu basira ko fahimtar abubuwa, amma ba haka abun yake ba. Binciken ZAUREN FIQHU ya gano cewar Tabar WEEWI tana sanya kwakwalwar 'Dan Adam ta rika yi masa tsallake ne.

Misali: Kamar kana so ka tuna abinda ya faru na kwana biyar da suka gabata, to sai Kwakwalwarka ta tsallake ta tuno maka da abinda ya faru tun shekaru 20 ko talatin da suka wuce..

Sinadarin THC dake cikin WEEWI yayi mutukar kamanceceniya da wani sinadarin da kwakwalwa take karbar sakonni dashi, ta yadda idan ya makale ajikinta yana iya sauyata. wannan yasa idan suka riga suka saba da juna, Kwakwalwar ba zata iya yin aikinta ba, dole sai dashi. Kuma bata iya bambancewa atsakanin sinadarin na weewi da kuma ainahin nata sinadarin.

Weewi tana haifar da Ciwon Qirji, Sankarar kwakwalwa (brain cancer) Sankarar Hunhu (Lung cancer) Taruwar Majinar Qirji wacce take toshe numfashi, Haukatar da tunani, etc.

Sannan Uwa-Uba tana haifar da hauka da juyewar Kwakwalwa, mutum dan Adam ya koma tamkar dabba.

Wannan yasa zaka ga mashayin Weewi ya tsugunna yana gaisar da Tumaki, ko kuma ka ganshi yana zaune cikin Qananan yara (wai shi atunaninsa shi kankanin yaro ne). Ko kuma ka ganshi haka kawai ya fashe da kuka ko dariya.

HUKUNCINTA TA FUSKAR ADDINI :

Manzon Allah (saww) yace "DUK ABINDA KESA MAYE (BUGARWA) SHIMA GIYA NE, KUMA DUKKAN ABINDA KE SANYA MAYE HARAMUN NE".

Ya kamata mu fahimci cewa duk da cewa mutanen lokacin Manzon Allah (saww) basu shan Weewi sai dai sauran abubuwan maye irin su Giya, Tsimi, etc. to amma ya riga ya game hukuncin cewa duk abinda ke sanya maye shima giya ne. Wannan ya hada da kwayoyi, Cocaine, Weewi, Shalisho, da duk qani abinda ke sanya maye.

Anan zamu tsaya da fatan Allah ya kiyayemu daga shan kayan maye, damu da dukkan zuriyarmu, wadanda Allah ya jarabcesu da shanta kuma Allah ya shiryesu ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (01-05-2015).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI