GIRMAN KAI RAWANIN TSIYA!!!
JUBLAH BN AL-AIHAM wani Sarki ne daga sarakunan Yankin Ghassan. Hasken Musulunci ya ratsa zuciyarsa har ya Musulunta. Sannan sai ya rubuta wasika zuwa ga Khalifan Musulunci na wannan lokacin (Zamanin Sayyiduna Umar bn Al-Khattab ne -rta-) yana sanar dashi game da Musuluntarsa, kuma yana neman idan anyi masa izini zai zo har Birnin Madeena (wato Headquarter).
Da Sayyiduna Umar (ra) ya karanta wasikar nan yayi farin ciki mutuka sosai. Hakanan sauran Jama'ar Musulman dake tare dashi (wato Sahabbai) duk sunyi Farinciki mai girma.
Sai Sayyiduna Umar (ra) ya rubuta tasa wasikar zuwa gareshi cewa : "KAZO GAREMU. KANA DA IRIN HAKKIN DA DUK MUKE DASHI, KUMA DUK HAKKIN DAKE KANMU KAIMA YANA KAN KA".
Shikenan sai ga Sarki Jublah ya taho tare da Sojoji dari biyar (500) akan dawakai suna yi masa rakiya.
Yayin da suka kusanto Birnin Madeena sai Jublah ya tsaya ya chanza Tufafinsa. Ya sanya wasu Tufafin Sarauta irin na Qasaita.. Tufafi ne wadanda aka yi musu ado da Zinare, aka ci bakinsu da zinare. Sannan ya dora kambin Sarauta akansa. Wata Hula ce wacce aka yi mata ado da Jauhari kala kala. Sojojin nasa ma suka sanya Tufafi irin na alfahari da Qasaita.
Yayin da suka shigo cikin Birnin Madeena, babu wani mutumin da ya saura sai da kowa ya fito don kallonsa. Har Qananan yara da Matan aure!!
Yayin da ya shigo wajen Sayyiduna Umar (ra) sai yayi masa maraba kuma ya kusanto dashi awajen Zamansa.
Yaci gaba da zama har lokacin aikin Hajji yayi. Sai suka tafi aikin Hajji tare da Sayyiduna Umar (ra).
Yazo Dakin Allah yana Tawafi sai wani Bawan Allah daga Qabilar Banu Fizarah ya taka masa Kwarjallensa (wani abu ne suke daurawa mai kama da Zani, Kuma shi nasa har jan Qasa yakeyi saboda Girman kai).
Sarki Jublah da ya waiwayo ya kalli mutumin nan sai ya Kwasheshi da Mari, har sai da hancinsa ya fashe yana tsiyayar da jini!
Mutmin nan shima ransa ya baci Don haka bai yi Qasa a gwiwa ba, sai ya kai Qarar sarkin nan wajen Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ra).
Sayyiduna Umar ya aika aka kirawo sarkin nan ya tambayeshi cewa : "Ya kai Jublatu mai yasa ka Mari dan uwanka Musulmi awajen Tawafi har ka fasa masa hanci?"
Sai yace "Kwarjallena ya taka min.. Ba don alfarmar Dakin Ka'abah ba, da sai na sare Wuyansa!".
Sai Sayyiduna Umar (ra) yace "To yanzu ka amsa laifinka kenan. Ko dai ka nemi yardarsa har ya yafe maka, ko kuma in sanyashi ya rama marinsa akan fuskarka!".
Sai Jublah yace "Yanzu yayi ramuko akaina, ni ina Matsayin Sarki, shi kuma Talaka?"
Sayyiduna Umar yace "Kwarai kuwa Ya kai Jublah. Domin Musulunci ya riga ya dadaita tsakanin kai dashi.. Ba zaka ta'ba finsa da komai ba, sai dai da tsoron Allah".
Sai Jublah yace "In dai hakane to ni zan koma addinin Nasaara (Kirista)".
Sai Sayyiduna Umar ya tuno da abinda Manzon Allah (saww) ya riga ya fada cewar "DUK WANDA YA CHANZA ADDININSA TO KU KASHESHI. Don haka idan ka koma addinin Nasaara zan fille wuyanka".
Sai yace "Ya Amiral Muminina, ina so ka jinkirta min zuwa gobe".
Sai Sayyiduna Umar ya bashi damar hakan.
Shi kuwa wannan sarki cikin dare ya tsere tare da Sojojinsa, ya tafi Birnin Qustantaniyyah (Babbar daular Kiristanci awancan lokacin) yaje ya shiga addininsu".
Chan ya zauna zamani mai tsawo. Yayin da zamani yayi nisa, duk dadin duniyar da yake ji ya gushe daga gareshi, Sai tsufa sai wahala.. Kuma sai ya rika tunowa da lokacin da yake Musulunci..
Yana tuna dadin Sallah da azumin nan da yayi alokacin Musuluncinsa, sai nadama ta kamashi bisa barin addinin Musuluncin da yayi, da kuma shirkar da ya shiga ta kiristanci.
Sai ya rika kuka yana waqa yana cewa:
"Madaukaka sun shiga addinin Nasaara don gujewa Mari kwalli daya tal! Gashi kuma babu ciwo gareta da ace nayi hakuri.
"Ya Kaichona, ina ma mahaifiyata bata haifeni ba! Inama da na dawo kan maganar da Umaru ya gaya min".
"Wayyo ni! Inama da ache ni Makiyayin dabbobi ne, ina yawo acikin Kabilun Rabee'atu da Mudhar!"
"Wayyo ni, inama da ache nine mafi Talauci acikin Mutanen Qasar Sham baki daya, Na kurumce na makance ina zaune acikin mutanena!"
Wannan Nadamar da yayi ba tayi masa amfani ba. Domin kuwa bai gushe dai acikin kafircinsa ba, Har ya rasu bisa wannan addinin Kiristancin.
Yanzu haka yana chan yana cin wuta acikin Qabarinsa ta sanadiyyar wannan GIRMAN KAN da yayi wa Shari'ar Allah Ubangijin Talikai baki daya.
Zauren Fiqhu : 'Yan uwa mu guji girman kai.. Shine rawanin Tsiya. Rawanin Talauci, Rawanin Qaskanci. Duk wanda ya daurashi to sai ya hallaka!
Ya Allah ka kiyayemu daga sharrin Zukatanmu, ka kyautata karshenmu. Aaameen.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (02-02-2016).
Ameen Thumma Ameen. Allah Yasaka Malam
ReplyDelete