MU SAN ANNABINMU (09)

Da Sunan Allah Mai rahama mai jin kai. Salati da amincinsa su tabbata bisa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da dukkan Magoya bayansa.

Wannan shine darasu na 9 acikin tarihin Shugaba (saww) wanda ke zuwa muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp.

HARBUL FUJJAR
******************
Bayan Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya cika shekaru ashirin (20) aduniya, wani Yaqi ya barke atsakanin Larabawa. Wato Quraishawa da Banu Kinanah ne suka ha'du suka yaqi wata Qabila mai suna "Qaisu 'Eelan".

Annabi (saww) ya halarci wajen wannan yaqin alhali yana matashi, yaje tare da baffaninsa 'ya'ysn Abdul Muttalib yana kawo musu kibiyoyin harbi. Amma dai daga karshe yaqin ya Qare da sulhu atsakanin Qabilun.

An kira wannan yaqin da sunan "Harbul Fujjar" ne saboda an yishi ne acikin watanni masu alfarma, wadanda ba'a saba yin yaqi acikinsu ba.

HILFUL FUDHUL

Bayan kammala Yaqin nan na Harbul Fujjar sai Quraishawa suka ha'du sukayi taro agidan wani da ake kira Abdullahi bn Jud'an At-Taimiy, suka Qulla alkawari atsakaninsu cewa daga yanzu zasu rika taimakon duk wanda aka zalunta akan hakkinsa, har sai sun karbi masa hakkinsa koda daga wajen waye.

To wannan alkawarin da suka yiwa junansu shi ake kira da suna "Hilful Fudhul". Annabi (saww) yana daga cikin wadanda suka halarci wajen kuma suka dauki wannan alkawarin. Kuma bayan Annabta yakan ce "Da za'a kira irinsa acikkn musulunci da sai na amsa".

Domin hakika irin wannan hadin kan yana kira ne zuwa ga fifiko. Haka Annabinmu (saww) ya taso cikin kyawun halaye da dabi'u masu tsarki, wani abu irin na dau'da da wautar jahiliyyah bai ta'ba shafarsa ba. Allah ya tsarkakeshi ya fifitashi kuma ya tanadeshi domin rahama ga dukkan talikai (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

An gabatar da karatun a ZAUREN FIQHU WHATSAPP ranar (05/03/1440 13/11/2018). 07064213990

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI