TAFKIN AL KAUTHARA

TAFKIN ALKHAUTHARA Yana daga cikin manyan abubuwan ni'ima na lahira wadanda Allah ya tanadar wa Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) domin girmamawa gareshi da al'ummarsa.

Acikin hadisai da dama Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi bayanin siffofin yadda tafkin yake, da kuma wadanda zasu sha daga gareshi.

Misali hadisin Sayyiduna Abdullahi bn Umar (radhiyallahu anhuma) wanda yace Manzon Allah (saww) yace :

"Tafkina (fa'dinsa) kamar nisan tsakanin Adanin da Amman, yafi Qankara sanyi, yafi zuma zaqi, kuma yafi dadin Qamshi fiye da Almiski.

Kofunansa  kamar yawan taurari, wanda yasha daga gareshi ba zai Qara jin kishirwa ba har abada. Farkon mutanen da zasu fara gangarowa gareshi sune talakawan Almuhajirun.

Sai wani yace "Su wanene Ya Rasulallah?!".

Sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "Sune wadanda gashin kansu yake da Qura-qura, fuskokinsu suke dauke da alamar wahala, tufafinsu yana da datti, ba'a bude Qofa saboda su (idan sun halarci waje). Kuma ba'a aura musu mata masu gata.

"Sune wadanda ke bayar da dukkan hakkokin dake kansu, amma basa karbar dukkan hakkokinsu (wato suna yin biyayya ga shugabanni, kuma suna hakuri bisa danne hakkokinsu da akeyi).

ADUBA :

MUSNADU AHMAD (Juzu'i na 5 shafi na 275).

Ya Allah ka gafarta mana zunubanmu baki daya don falalarka da rahamarka, Ka shayar damu ruwan tafkin Annabinmu (saww) ka sanyamu cikin aljannarka firdausi ba tare da hisabi ko uqubah ba. Ameen.

Kuma wannan hadisin yana nuna falalar da talakawa suke dashi akan masu hannu da shuni, mutukar sun kiyaye dokokin Allah. Allah yasa mu dace ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (24/07/2019 21/11/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI