ADDU'AR SAMUN BIYAN BUKATU

ADDU'AR SAMUN BIYAN BUKATU :
************************************
Ku bude Kunnuwanku ku saurara. Addu'a ce ta Musamman wacce Annabi (saww) yayi ma 'Yarsa (Nana Fatimah) Wasiyyah da ita.

Sayyiduna Anas bn Malik (rta) ya ruwaito cewa watarana Manzon Allah (saww) yace ma 'Yarsa Nana Fatimah (r.a.):

"MAI ZAI HANAKI KI SAURARI ABINDA ZANYI MIKI WASIYYAH DASHI?

KI RIKA FA'DA IDAN KIKA WAYI GARI, DA KUMA IDAN KIN YAMMANTA :

"YA HAYYU YA QAYYOUM BI RAHMATIKA ASTAGHEETHU, ASLIHLEE SHA'ANEE KULLAHU WALA TAKILNEE ILA NAFSEE TARFATA 'AININ".

MA'ANA : Ya Rayayyen Sarki, Ya Madawwami (Tsayayye akan lamarin bayinsa) da rahamarka ne nake neman Taimako. Ka kyautata min sha'anina baki dayansa. Kar ka dogarar dani zuwa ga kaina.

#Imamun Nisa'iy ne da Bazzaar suka ruwaitoshi da Ingantaccen Isnadi.

ZAUREN FIQHU :
*****************
Wannan addu'a ce ta musamman wacce in sha Allahu Za'a samu biyan bukatu idan dai ana yinta da kyakyawar Niyyah tare da cika ladubban addu'a.

Idan kana fama da rikicewar al'amura, ko rashin fahimtar karatu, ko kuma rashin jin dadi agidan Mijinki, ko kuma Mijin aure kike nema, to sai arika yin wannan addu'ar.

Allah yasa mu dace. Aaameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (03-04-2016).

Comments

  1. ina farin ciki da wanna lokaci allah ya kara muna kariya a duk lokacin da (yar) makaranta ko (dan)makaranta ya dinga samu nasara da fahimta ako wani lokaci ya sami kansa yana cikin masu nasaran cin jarubawa ,allah ya muna kariya ameen.

    ReplyDelete
  2. Very Nice Post. I am very happy to see this post. Such a wonderful information to share with us. For more information visit here Blogger.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI