BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
**************************************
Anan ZAUREN FIQHU Muna yawan samun tambayoyi akan wannan Mas'alar daga bangarorin Maza da mata. Amma in sha Allahu yanzu zanyi bayani daidai gwargwadon iko.

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Ina fatan zaku gafarceni. Zanyi bayani dalla dalla (duk da cewar akwai nauyi sosai) to amma abu ne wanda ya shafi addini. Kuma bangaren tsarki ne wanda sai dashi ibadah zata yiwu.

Maniyyi da Maziyyi suna da bambanci ta bangarori guda uku kamar haka:

1. Bambanci a yanayin Siffarsu.

2. Bambanci ayanayin da ake ji bayan fitarsu.

3. Bambanci a bangaren hukuncinsu.

1. SIFFOFINSU
*****************
Manzon Allah (saww) shi da kansa yayi bayanin yadda siffarsu take yayin da yake bada amsa bisa tambayar da Sayyidah Ummu Sulaym tayi masa.

Yace : "SHI DAI MANIYYIN NAMIJI, FARI NE KUMA YANA DA KAURI. SHI KUMA MANIYYIN MACE, FATSI FATSI NE, KUMA TSINKAKKE NE (BASHI DA KAURI).

(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).

Akan wannan ne malamai sukayi Qarin bayani cewa Shi maniyyin Namiji yana Qamshin Furen dabino ne. Kuma yana fita ne tare da zunkudar junansa. (wato yana fita da Qarfi). Shima na macen haka yake.

Kuma in dai maniyyi ya fita daga Mace ko Namiji, acikin barci ko afarke, to yana Wajabta wanka.

Sai dai wadanda suke tare da Larura ko jinya, ko kuma ta dalilin faduwa daga sama, har maniyyi yakan fita daga garesu ba tare da motsuwar sha'awar komai ba, to wannan ba ya karya azumi kuma ba ya wajabta wanka.

Shi kuma MAZIYYI duk kala daya ne na mata da na Mazan. fari ne shi garai garai. Kuma yana fitowa ne bisa dalilin motsawar sha'awar Jima'i. Ta dalilin Kallo, ko shafa, da Tunanin Jima'i.

2. BAMBANCI YAYIN FITARSU:

Shi Maniyyi yana fita ne yayin da sha'awa ta kai Kololuwa, kuma akan samun mutuwar Jiki, har tsattsafowar gumi bayan fitarsa.

Shi kuma Maziyyi yana fita ne yayin motsawar sha'awa kadai. Kuma ba'a samun mutuwar jiki bayan fitarsa.

3. BAMBANCI A HUKUNCINSU:

Fitar Maniyyi tana wajabta wanka, ita kuma fitar Maziyyi bata wajabta wanka. Sai dai Mutum zai je ya wanke al'aurarsa baki daya.

Malamai sunyi sabani akan Shin Maniyyi Najasa ne, ko ba najasa bane. Amma shi Maziyyi kowa ya yarda cewa shi NAJASA ne.

MAGANAR QARSHE:

Maniyyin Maza: Fari ne yana da kauri da yauki.

MANIYYIN MATA: Fatsi ne, bashi da kauri, kuma yana da yauki yauki.

Ana yin wanka saboda fitarsa. Kuma Malaman Malikiyyah sunce Shi maniyyi Najasa ne.

MAZIYYI : Na maza da Mata duk iri daya ne. Kuma fari ne tsinkakke. Garai garai yake kamar ruwan sha.

Yana karya alwala, kuma ana wanke al'aura baki dayanta sabosa fitarsa. Kuma za'a wanke tufafin da ya taba.

WADIYYI : Yana fita ne akarshen fitsari. hukuncinsu daya da fitsarin. Za'a wankeshi ne kawai.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (4)

Anyi izini zaku iya tura ma wadansu domin su amfana. Saboda mas'alar tana damun mutane da yawa.

ZAUREN FIQHU 07064213990 (12-08-2015)

Comments

  1. Jazakallah khairan. Allah ya kara daukaka da basira Malam

    ReplyDelete
  2. Jazakallah khairan. Allah ya biya bukata duniya da lahira

    ReplyDelete
  3. Allah ya kara muku cigaba... AMEEN

    ReplyDelete
  4. Allah yasa Ka da alheri Malan, Dan Allah Malan a saka ni a whatsapp group, 07032837873

    ReplyDelete
  5. Allah yasa Ka da alheri Malan, Dan Allah Malan a saka ni a whatsapp group, 07032837873

    ReplyDelete
  6. Allah ya saka da alkhairi.Malam Dan Allah asa number Na whatsApp group,08139377573 Nagode.

    ReplyDelete
  7. Na yi imani da wanda ya mallaki 100% na zuciyarka ya cancanci yaƙin. Haka ne, ina alfahari saboda ban taɓa bin shawara mai kyau daga iyayena ba lokacin da nake son yin aure. Akwai yakin tsakanin iyalinmu biyu sannan mijina ya kasance jaririn uwarsa, 'yan uwansa sunyi amfani da shi da yawa wanda ya yanke hukunci ba tare da tuntube su ba. Abinda ya mamaye ni shine lokacin da dan shekaru 36 ya nemi iyayensa da wasu dangi su yarda kafin su gana da kowa da kowa, mafi munin abin da ya faru lokacin da aka umurce shi ya kawo ni zuwa ƙasarsu a Rampart, New Orleans, yana da haɗari don karɓar wannan gayyatar.Gamar tsakanin iyalanmu ya fara lokacin da ya karshe (wannan kimanin shekaru 4 da suka wuce), iyalinsa sun ba da wasu ka'idoji idan yana da matata (muna zama tare da su), na yi fushi lokacin da miji yarda da farin ciki da yanayin su (don haka mahaukaci). Iyalanmu sun yi tawaye kuma sun bukaci ya kamata in rabu da shi nan da nan.Na yanke shawarar ba shi harbin karshe kamar mutum wanda ya riga ya dauki 100% na zuciyata, na dauki haɗari na tafiya ta ruhaniya tare da su ta hanyar tuntuɓar Doctor Sharaja ta sharajasid @ Gmail.com, Ban sani ba amma mahaifin ruhaniya ya rigaya ya san zan shawarce shi. Da farko dai ya gaya mani hatsarin da nake ciki da kuma yadda miji ya zama bautar tun lokacin da aka haife ni, yadda suke ci gaba da kwakwalwa ta wanke shi don yin abin da suke so. Kamar yadda abin da mutum yake gani a hankali kawai, na gane cewa babu wanda ya ga abin da na gani a cikin mijina kuma wancan ne dalilin da ya sa na yi amfani da taimako na SHARAJA SHIRYA don cire shi daga cikin wahala. Idanunsa inda aka bude ta SHARAJA SID a karo na farko, iyalinsa sun ƙaunace ni kuma sun ba da duk bukatunmu, iyalanmu sun san zaman lafiya tun bayan ƙaunar da aka yi. Yana da shekaru 2 bayan ƙauna da mijina ya ci gaba da inganta kowace rana ba tare da tsangwama daga iyalinsa ba. Na jira tsayi sosai don raba wannan yanki mai ban mamaki. Na gode da lokacinka da kuma SHARAJA SID. Na san shi ta hanyar karatun wasu shaidun ban mamaki game da blogs .. rubutu firist sharajasid ++ (234) 9066-376197

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI