ZIKIRINMU NA YAU (25/10/2017)
ZIKIRINMU NA YAU (25/10/2017)
*********************************
Hadithi daga Ɗalqu bn Habeeb yace "Wani mutum yazo wajen Abud Darda'i (rta) yace masa "Ya kai Abud Darda'i! Hakika gidanka ya Qone!".
Sai Abud Darda'i yace "A'a bai Qone ba! Allah ba zai ta'ba yin haka ba, saboda wasu kalmomi da najisu daga wajen Manzon Allah (saww).
Duk wanda ya fa'desu a farkon wuni, babu wata musibar da zata sameshi har sai ya yammanta. Kuma duk wanda ya fa'desu a Qarshen wuni, babu wata musibar da zata sameshi har sai ya wayi gari :
اللهم أنت ربي لا إله إلا أنت ، عليك توكلت وأنت رب العرش العظيم. ما شاء الله كان وما لم يشأ لم يكن ، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم، أعلم أن الله على كل شيء قدير و أن الله قد أحاط بكل شيء علما ، اللهم إني أعوذ بك من شر نفسي و من شر كل دابة ربي آخذ بناصيتها، إن ربي على صراط مستقيم >>
Allahumma anta Rabbee la ilaha illa anta, 'Alaika tawakkaltu wa anta rabbul 'arshil 'azeem.
Ma sha Allah kana wama lam yasha' lam yakun, wala haula wala quwwata illa billahil 'aliyyil 'azeem.
A'alamu annal Laha 'ala kulli shay'in qadeerun wa annal Laha Qad ahaata bikulli shay'in 'ilman.
Allahumma innee a'udhu bika min sharri nafsee wa min sharri kulli dãbbatin Rabbee ãkhizun bi nãsiyatiha inna Rabbee 'ala Sirãtin Mustaqeem.
FASSARA : Ya Allah kaine Ubangijina babu wani abin bautawa da gaskiya fache kai. Gareka na dogara, kuma kaine Ubangijin al'arshi mai girma.
Abinda Allah yaso shi ke kasancewa, abinda kuma bai so ba, bazai ta'ba yiwuwa ba. Kuma babu wata dabara kuma babu wani Qarfi sai da Allah Madaukaki mai girma.
Na sani hakika Allah shi keda iko akan komai, Kuma cewa hakika Allah ya kewaye komai da iliminsa.
Ya Allah ina neman tsarinka daga sharrin kaina da kuma sharrin duk wata hlitta wacce Ubangijina ne yake rike da akalarta. Hakika Ubangijina yana bisa tafarki Madaidaici.
ibnus Sunnee ne ya ruwaitoshi acikin 'AMALUL YAUMI WAL LAYLA, amma acikin isnadinsa akwai Aglabu bn Tameem, wanda malaman hadithi sunyi magana akansa.
Wannan addu'ar Malamai sun yarda da ita sosai. Kuma tana aiki sosai ga duk wanda yake yinta zai riski falalarta in sha Allahu.
Ibnul Qayyim Aljawziyyah ya kawota acikin Al-Wabilus Sayyib acikin fasalin farko dake bayanin zikirai na safe da yamma.
Duk mai bukatar kariya daga Allah da kuma samun taimakon Allah acikin harkokinsa, to ya riki addu'a tare da gaskatawa.
Mai bukatar wankin zuciya da samun farin ciki aduniya da lahira, to ya rike zikirin Allah ako yaushe. Zai ga abun mamaki cikin kulawar Ubangiji.
DAGA ZAUREN FIQHU (25/10/2017 06/02/1439).
Comments
Post a Comment