Posts

Showing posts from February, 2018

ANNABI BAHRUN NADA (SAWW)

ANNABI BAHRUN NADA (SAWW) ********************************* Qaisu bn Nu'uman (ra) yace : Lokacin da Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yake tafiya da Sayyiduna Abubakrin domin yin hijirah, sun wuce ta kusa da wani Bawa yana kiwon dabbobi. Sai suka tambayeshi ki zasu samu Nono su sha?. Sai yace "Babu wata akuya awajena wacce za'a iya tatsa daga gareta, Sai dai ga wata Raquma nan wacce ta dauki ciki tun afarkon hunturu, Kuma riga ta fita. Babu sauran nono gareta". Sai Annabi (saww) yace masa "KIRAWOTA". (Bayan zuwanta) sai Annabi (saww) ya sanya mata dabaibayi, ya shafi hantsarta yayi addu'a har sai da Nonon yazo. Sayyiduna Abubakrin (ra) ya kawo mazubi, Annabi (saww) ya tatsa ya shayar da Abubakrin din. Ya sake tatsa ya shayar da Makiyayin, Sannan ya tatsa yasha. Sai wannan makiyayin yace masa "Don Allah wanene kai? Domin wallahi ban ta'ba ganin tamkarka ba tunda nake". Sai Manzon Allah (saww) yace "SHIN KANA

GUZURIN SAFIYA (01)

Ya Ubangiji hakika mun wayi gari muna masu imani da kadaitakarka, da kuma Manzancin Annabinka Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam). Muna cikin masu mika godiya da kirari gareka bisa dukkan ni'imominka na fili da boye.. Hakika bamu isa mu gode maka da irin godiyar da ta chanchanta gareka ba. Muna cikin masu dogaro dakai da kuma neman taimakonka.. Hakika Kaine Fiyayyen Majibinci, Fiyayyen Mataimaki, Kuma fiyayyen abin dogaro. Hakika Kaine Mai yin baiwa ga bayinka ba don sun chanchanta da ita ba, sai dai don falalarka da rahamarka garesu. To Ya Allah muna Kamun Qafa da fiyayyen Masoyinka, da dukkan abinda yafi soyuwa gareka, Ka cika ni'imominka akanmu, Ka bamu lafiyar fili da boye, Ka suturcemu da bargon suturarka, Kayi mana arzikin duniya da lahira. Ameen. Salatinka mafi girma da amincinka mafi cika su tabbata ga Fiyayyen Bayi,  Annabi Muhammadu kenan tare da iyalan gidansa hasken al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya, da dukkan Salihan bayinka har zuwa

FATIMAH BINTU ASADIN ALHASHIMIYYAH

FATIMAH BINTU ASAD (RTA) ***************************** FATIMAH BINTU ASAD BN HASHIM BN ABDI MANAAF, ALQURASHIYYAH ALHASHIMIYYAH... (Allah shi Qara yarda da ita). Mahaifiyar Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib dashi da 'Yan uwansa Ja'afar bn Abi Talib da 'Aqeel bn Abi Talib (rta). Ita ce wacce ta rike Manzon Allah (saww) kuma ta kula dashi alokacin da yake hannun baffansa Abu Talib. Ta hidimtawa Ma'aiki (saww) tsawon rayuwarsa. Ta musulunta tun afarkon lamari. Kuma tayi hijira zuwa Madeenah, kuma a Madeena dinma ta rasu. Imamuz Zuhriy yace ita ce farkon Bahashimiyar da ta haifi Bahashime kuma Mijinta ma Bahashimi. Kuma ita ce Farkon Bahashiyar da Haifi wanda ya zamto Khalifan Musulunci. Bayan ita sai Fatimah 'Yar Manzon Allah (saww) wacce ta haifi Sayyiduna Hasan (ra).sai kuma Zubaidah Matar Khalifah Harunar Rasheed wacce ta haifi Khalifah Al Ameen. Lokacin da Fatimah bintu Asad (ra) ta rasu,  Manzon Allah (saww) yayi mata likkafani ne da rigarsa mai albarka.. Kuma d