FATIMAH BINTU ASADIN ALHASHIMIYYAH

FATIMAH BINTU ASAD (RTA)
*****************************
FATIMAH BINTU ASAD BN HASHIM BN ABDI MANAAF, ALQURASHIYYAH ALHASHIMIYYAH... (Allah shi Qara yarda da ita).

Mahaifiyar Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib dashi da 'Yan uwansa Ja'afar bn Abi Talib da 'Aqeel bn Abi Talib (rta).

Ita ce wacce ta rike Manzon Allah (saww) kuma ta kula dashi alokacin da yake hannun baffansa Abu Talib.

Ta hidimtawa Ma'aiki (saww) tsawon rayuwarsa. Ta musulunta tun afarkon lamari. Kuma tayi hijira zuwa Madeenah, kuma a Madeena dinma ta rasu.

Imamuz Zuhriy yace ita ce farkon Bahashimiyar da ta haifi Bahashime kuma Mijinta ma Bahashimi. Kuma ita ce Farkon Bahashiyar da Haifi wanda ya zamto Khalifan Musulunci. Bayan ita sai Fatimah 'Yar Manzon Allah (saww) wacce ta haifi Sayyiduna Hasan (ra).sai kuma Zubaidah Matar Khalifah Harunar Rasheed wacce ta haifi Khalifah Al Ameen.

Lokacin da Fatimah bintu Asad (ra) ta rasu,  Manzon Allah (saww) yayi mata likkafani ne da rigarsa mai albarka.. Kuma da hannayensa masu albarka ya sanyata acikin Qabarinta. Kuma ya shiga ya kwanta acikin Qabarin sannan yayi mata addu'a.

Yana cewa "YA ALLAH KA GAFARTA MA BABATA FATIMATU 'YAR ASAD DOMIN HAKKIN ANNABINKA DA ANNABAWAN DA SUKA ZO KAFIN NI".

Abdullahi bn Abbas (rta) yace da Sahabbai suka tambayi Manzon Allah (saww) cewa "Mun ga ka aikata wano abu wanda baka ta'ba yi ma wani ba".

Sai Manzon Allah (saww) yace "BAYAN ABU TALIB ITA CE MAFI TAIMAKO GARENI. KUMA NA SANYA MATA RIGATA NE DOMIN A TUFATAR DA ITA DAGA KAYAN GIDAN ALJANNAH. KUMA NA KWANTA ACIKIN QABARINTA NE DOMIN A SAUKAKA MATA AZABAR QABARI".

Allah ya saka mata da alkhairi bisa hidimar da tay ma Annabinmu (saww). Allah shi bamu albarkar masu albarka ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU (01-02-2018 14-05-1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI