ANNABI BAHRUN NADA (SAWW)

ANNABI BAHRUN NADA (SAWW)
*********************************
Qaisu bn Nu'uman (ra) yace :

Lokacin da Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yake tafiya da Sayyiduna Abubakrin domin yin hijirah, sun wuce ta kusa da wani Bawa yana kiwon dabbobi. Sai suka tambayeshi ki zasu samu Nono su sha?.

Sai yace "Babu wata akuya awajena wacce za'a iya tatsa daga gareta, Sai dai ga wata Raquma nan wacce ta dauki ciki tun afarkon hunturu, Kuma riga ta fita. Babu sauran nono gareta".

Sai Annabi (saww) yace masa "KIRAWOTA". (Bayan zuwanta) sai Annabi (saww) ya sanya mata dabaibayi, ya shafi hantsarta yayi addu'a har sai da Nonon yazo.

Sayyiduna Abubakrin (ra) ya kawo mazubi, Annabi (saww) ya tatsa ya shayar da Abubakrin din. Ya sake tatsa ya shayar da Makiyayin, Sannan ya tatsa yasha.

Sai wannan makiyayin yace masa "Don Allah wanene kai? Domin wallahi ban ta'ba ganin tamkarka ba tunda nake".

Sai Manzon Allah (saww) yace "SHIN KANA GANIN ZAKA 'BOYE MIN LABARINA, IN GAYA MAKA?".

Yace "Eh".

Sai yace "TO HAKIKA NINE MUHAMMAD MANZON ALLAH (SAWW)".

Sai Makiyayin yace "Kaine wanda Quraishawa suke cewa "Ya kauce hanya".

Sai Annabi (saww) yace "HAKIKA SU SUNA FA'DAR HAKA".

Sai Makiyayin yace "To Nidai na shaida cewa lallai Kai Annabi ne. Kuma na shaida cewa abinda kazo dashi Gaskiya ne. Kuma lallai babu wanda zai iya yin irin abinda kayi sai dai in Annabi ne. Kuma ni Mabiyinka ne". (wato zan bika mu tafi).

Sai Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace masa "HAKIKA KAI BA ZAKA IYA YIN HAKA AYANZU BA. AMMA IDAN KA SAMU LABARIN BAYYANATA KA TAHO GAREMU".

Imamul Baihaqiy ne ya ruwaitoshi acikin Dala'ilun Nubuwwah (Juzu'i na 2 shafi na 224-225).

Salatin Allah da amincinsa su tabbata agareka da iyalan gidanka Ya Abal Qasim, Abal Mu'azzami, Abaz Zahra'..

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (03-06-1439  18-02-2018).

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI