GUZURIN SAFIYA (01)

Ya Ubangiji hakika mun wayi gari muna masu imani da kadaitakarka, da kuma Manzancin Annabinka Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Muna cikin masu mika godiya da kirari gareka bisa dukkan ni'imominka na fili da boye.. Hakika bamu isa mu gode maka da irin godiyar da ta chanchanta gareka ba.

Muna cikin masu dogaro dakai da kuma neman taimakonka.. Hakika Kaine Fiyayyen Majibinci, Fiyayyen Mataimaki, Kuma fiyayyen abin dogaro.

Hakika Kaine Mai yin baiwa ga bayinka ba don sun chanchanta da ita ba, sai dai don falalarka da rahamarka garesu.

To Ya Allah muna Kamun Qafa da fiyayyen Masoyinka, da dukkan abinda yafi soyuwa gareka, Ka cika ni'imominka akanmu, Ka bamu lafiyar fili da boye, Ka suturcemu da bargon suturarka, Kayi mana arzikin duniya da lahira. Ameen.

Salatinka mafi girma da amincinka mafi cika su tabbata ga Fiyayyen Bayi,  Annabi Muhammadu kenan tare da iyalan gidansa hasken al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya, da dukkan Salihan bayinka har zuwa ranar sakamako.

DAGA ZAUREN FIQHU (29/05/1439 15/02/2018).

'YAN UWA DA FATAN AN TASHI LAFIYA...

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI