Posts

Showing posts from April, 2018

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (10)

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (10) ********************************** DA SUNAN ALLAH BUWAYI GAGARA-MISALI. SARKIN DA BASHI DA TAMKA, BAI HAIFA BA, KUMA BA HAIFARSA AKAI BA. Salati da aminci su tabbata su dawwama bisa Annabin da Allah ya aiko domin fitar da dukkan halittu daga duhun kafirci zuwa ga hasken Musulunci da imani. Da iyalansa da Sahabbansa da dukkan nagartattun bayi. Bayan alamomi masu girma wadanda muka ambata acikin rubutun Zauren Fiqhu na 1 zuwa na 9, sai kuma Alqiyamah ta Qara matsowa gab da afkuwarta.. Sai dai Allah Madaukakin Sarki shi ka'dai ya kebanta da sanin hakikar lokacin faruwarta. 'Boyewar da Ubangiji yayi ma hakikar lokacinta, tare da tsoratarwar da yake ma bayinsa game da ita, duk wannan ya nuni ne zuwa ga Girman lamarinta.. Idan Alqiyamah zata tsaya, ba wai shela akeyi ko sanarwa ba, Kawai ganinta za'ayi ta afku ba tare da tsammani ba.. Allah yace "BA ZATA ZO MUKU BA, FACHE LOKACI GUDA (BA TARE DA TSAMMANI BA). Kuma yace "LAMARIN ALQIYA

MADUBIN DUBAWA (055)

MADUBIN DUBAWA (55) ************************* Hakika wasu daga cikin 'Yan uwa da dangi suna da abin haushi.. Sukan kasance kullim cikin zarginka ko Kokarin ganin laifinka. Basu tuna alkhairinka kullim sai sharrinka suke nema.. Idan ma basu samu laifinka ba sai sun kirkiro sun lika maka. Kayi iyakan Kokarinka wajen ganin ka fita hakkinsu ta hanyar ziyartarsu ko kyautata musu amma ba zasu ta'ba kallon wannan ba, balle su gode maka. Kullum shaitan (L. A) yana zugaka yana gaya maka cewa ka dena kulasu, ko kuma ka rika gaba dasu kana rama irin Qiyayyar da suke maka, ko kuma ka yanke igiyar zumuncinka dasu.. To kar ka manta fa, Annabinka (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace : "DUK WANDA YAKE SO AJA KWANANSA KUMA A YALWATA MASA ARZIKINSA TO YA SADAR DA ZUMUNCINSA". Shin baka son albarkar rayuwa ne, ko kuma baka so Allah ya sanya albarka cikin Arzikinka???. Idan kuwa kana son haka, to mai yasa ba zakayi hakuri da halayensu ba? Mai yasa ba zakayi afuwa garesu ba

FIFIKON ANNABI AKAN

Da sunan Allah Mai Cikakken ikon da baya bukatar taimako. Salati da aminci su tabbata bisa Annabin Qarshe wanda Allah ya aikoshi don Jin Qan halittu da dukkan taimako. Tare da iyalan gidansa da Sahabbansa masu kaiwa kafirai farmaki cikin dare da yayin sammako, da dukkan Salihan bayin Allah har zuwa ranar sakamako. Kamar yadda Imam Jalaluddeen Assuyutiy (Allah ya rahamsheshi) ya fa'da acikin littafinsa AL KHASA'ISUL KUBRA, babu wata Mu'ujizah ko wani fifikon da Allah ya bama wani Annabi ko Manzo daga cikin Manzanni (alaihimus salam) fache sai da ya bama Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) irinta ko kuma mafificiyarta. Bari ma dai, wasu Malaman sun ce, dukkan wata baiwa wacce Allah yai ma Annabawa (alaihimus salam) ya tattara ya bama Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) baki dayansu. Acikin wannan darasin, Zauren Fiqhu zai kawo fassarar wasu daga darajojin da Allah Madaukakin Sarki ya kebanci Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) da