IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (10)

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (10)
**********************************
DA SUNAN ALLAH BUWAYI GAGARA-MISALI. SARKIN DA BASHI DA TAMKA, BAI HAIFA BA, KUMA BA HAIFARSA AKAI BA.

Salati da aminci su tabbata su dawwama bisa Annabin da Allah ya aiko domin fitar da dukkan halittu daga duhun kafirci zuwa ga hasken Musulunci da imani. Da iyalansa da Sahabbansa da dukkan nagartattun bayi.

Bayan alamomi masu girma wadanda muka ambata acikin rubutun Zauren Fiqhu na 1 zuwa na 9, sai kuma Alqiyamah ta Qara matsowa gab da afkuwarta.. Sai dai Allah Madaukakin Sarki shi ka'dai ya kebanta da sanin hakikar lokacin faruwarta.

'Boyewar da Ubangiji yayi ma hakikar lokacinta, tare da tsoratarwar da yake ma bayinsa game da ita, duk wannan ya nuni ne zuwa ga Girman lamarinta..

Idan Alqiyamah zata tsaya, ba wai shela akeyi ko sanarwa ba, Kawai ganinta za'ayi ta afku ba tare da tsammani ba.. Allah yace "BA ZATA ZO MUKU BA, FACHE LOKACI GUDA (BA TARE DA TSAMMANI BA).

Kuma yace "LAMARIN ALQIYAMAH BAI ZAMANTO BA, SAI DAI KAMAR QIFTAWAR IDO KO FIYE DA HAKA".

Lamarin Farko dai acikinta shine BUSAR QAHO.. Qaho ne wanda girmansa yafi na dukkan abinda ke doron Qasa.. Kuma yana cikin bakin wani Mala'ika ne (Israfeel) wanda aka kebanceshi da girman halittar jiki. Kamar yadda yazo a hadisi, girman kafadarsa ka'dai yafi nisan tafiyar shekaru 100.

Hakika wannan busar Qahon na tashin Alqiyamah, tamkar kiran sallah ne ga Sallah. Domin shine sanarwar faruwarta kuma yankewar rayuwar duniya kenan baki daya.

Ubangiji yace "RANAR DA ZAKU GANTA, DUK WATA MAI SHAYARWA ZATA SHAGALTA DAGA ABINDA TAKE SHAYARWA, KUMA DUK WATA MA'ABOCIYAR CIKI (JUNA BIYU) ZATA HAIFE ABINDA TAKE DAUKE DASHI. KUMA ZAKA GA MUTANE SUNA TANGA'DI KUMA BA ABIN MAYE SUKA SHA BA, SAI DAI AZABAR ALLAH MAI TSANANI CE".

Wannan fa ita ce Siffar Firgicin farko na ranar Alqiyamar. Da fatan Allah ya sanyamu cikin bayinsa amintattau.

Hakika lamarin tashin Alqiyamah da girma yake.. Shi yasa da kansa yake rantsuwa akan sha'aninta. Amma mu 'Yan Adam kamar bamu damu ba.

Ya Allah ka saukaka mana, ka yafe mana. Kayi mana rangwamen laifukanmu ka shafesu baki daya. Kayi mana rahama domin Kaine mafi Jin Qai ga bayinka.

An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp (3) ranar 29/04/2018 13/08/1439.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI