FIFIKON ANNABI AKAN
Da sunan Allah Mai Cikakken ikon da baya bukatar taimako. Salati da aminci su tabbata bisa Annabin Qarshe wanda Allah ya aikoshi don Jin Qan halittu da dukkan taimako. Tare da iyalan gidansa da Sahabbansa masu kaiwa kafirai farmaki cikin dare da yayin sammako, da dukkan Salihan bayin Allah har zuwa ranar sakamako.
Kamar yadda Imam Jalaluddeen Assuyutiy (Allah ya rahamsheshi) ya fa'da acikin littafinsa AL KHASA'ISUL KUBRA, babu wata Mu'ujizah ko wani fifikon da Allah ya bama wani Annabi ko Manzo daga cikin Manzanni (alaihimus salam) fache sai da ya bama Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) irinta ko kuma mafificiyarta.
Bari ma dai, wasu Malaman sun ce, dukkan wata baiwa wacce Allah yai ma Annabawa (alaihimus salam) ya tattara ya bama Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) baki dayansu.
Acikin wannan darasin, Zauren Fiqhu zai kawo fassarar wasu daga darajojin da Allah Madaukakin Sarki ya kebanci Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) dasu wadanda bai yi ma sauran Annabawa da Manzanni ba :
1. Yana daga kebantuwar darajarsa (saww) cewa Allah ya nuna masa Mala'ika Jibreelu (alaihis salam) acikin ainahin siffarsa wacce Allah ya halicceshi da ita.
2. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa Allah Madaukakin Sarki ya turo Mala'iku sun tsaga Qirjinsa sun fiddo zuciyarsa sun wanketa har sau biyu, alokacin Quruciyarsa da kuma daren Isra'i da Mi'iraji. Kuma Allah ya sanya Khatimin Annabta atsakanin Kafadunsa masu daraja (saww).
3. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa Allah ya karbi cetonsa akan baffansa Abu Talib an sassauta azaba gareshi.
4. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa Allah ya tafiyar dashi daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Qudus acikin wani dare, sannan ya tafiyar dashi zuwa cikin sammai bakwai har ma gaba da nan, ya keta dubban hijabai kuma ya gana da mahaliccinsa (SWT).
5. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa alokacin da Allah ya tattara masa dukkan Annabawa da Manzanni (as) a masallacin Qudus sunyi imani dashi kuma ya wuce gaba yaja su Sallah amatsayin Limaminsu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
6. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa shi Allah ya bama Alqur'ani amatsayin littafi, daftarin shari'a, Kuma Mu'ujizah mai girma wacce ta tattaro fasahar harshe da Qurewar tsari wajen jerin kalmomi da ma'anoni.
7. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa littafinsa (Alqur'ani) Mu'ujizarsa bata Qarewa kuma bata Qurewa har zuwa tashin Alqiyamah.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1) {20/07/1439 06/04/2018}.
Comments
Post a Comment