MADUBIN DUBAWA (055)

MADUBIN DUBAWA (55)
*************************
Hakika wasu daga cikin 'Yan uwa da dangi suna da abin haushi.. Sukan kasance kullim cikin zarginka ko Kokarin ganin laifinka. Basu tuna alkhairinka kullim sai sharrinka suke nema.. Idan ma basu samu laifinka ba sai sun kirkiro sun lika maka.

Kayi iyakan Kokarinka wajen ganin ka fita hakkinsu ta hanyar ziyartarsu ko kyautata musu amma ba zasu ta'ba kallon wannan ba, balle su gode maka.

Kullum shaitan (L. A) yana zugaka yana gaya maka cewa ka dena kulasu, ko kuma ka rika gaba dasu kana rama irin Qiyayyar da suke maka, ko kuma ka yanke igiyar zumuncinka dasu..

To kar ka manta fa, Annabinka (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace : "DUK WANDA YAKE SO AJA KWANANSA KUMA A YALWATA MASA ARZIKINSA TO YA SADAR DA ZUMUNCINSA".

Shin baka son albarkar rayuwa ne, ko kuma baka so Allah ya sanya albarka cikin Arzikinka???. Idan kuwa kana son haka, to mai yasa ba zakayi hakuri da halayensu ba? Mai yasa ba zakayi afuwa garesu ba?. Mai yasa ba zaka ci gaba da yin alheri garesu ba???.

Arzikinka ko rufin asirin dake gareka, Shin ba Allah ne ya baka ba???. Shi Allah din a kullum kana cikin sa'bonsa amma bai yanke arzikinka ba, Kuma bai dena yin kyautuka gareka ba... Afuwa yake yi maka.. Yana shafe laifukanka.. Bai Quntata maka saboda laifukanka ba domin SHI Afuwwun Ghafurun ne.

Manzon Allah (saww) yace : "MAI YANKE ZUMUNCI BA ZAI SHIGA ALJANNAH BA".

Shin laifin da 'uan uwanka suke maka ya kai ka rasa aljannah dominsa??. Shin ka zabi shiga wuta maimakon hakuri da laifin dan uwanka??... Haba 'Dan uwa, Ka sake tunani..

Allah mai rahama yana jin tausayin masu tausayi.. Kuyi ma 'yan uwanku afuwa ku yafe musu sai Mala'iku su rika nema muku gafara.. Kuma Allah yai muku rahama..

Wannan nasiha ce daga Zauren Fiqhu 07064213990 (27/07/1469 13/04/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI