DARAJOJIN AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM)
Wannan shine kashi na hudu acikin bayanin darajoji da falalar iyalan gidan Annabin Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) acikin jerin darussan Zauren Fiqhu : Sayyiduna Usamah 'dan Zaidu (rta) yace "Watarana na kwankwasa kofar gidan Annabi (saww) akan wasu bukatu, Sai (Naji yana cewa) : "WADANNAN 'YA'YANA NE, KUMA 'YA'YAN 'DIYATA. YA ALLAH NI INA SONSU KAIMA KASO SU KUMA KASO DUK MAI SONSU". (Imamut Tirmidhiy ne ya ruwaito). Imamu Muslim ya fitar da wani hadithi acikin Sahih nasa, juzu'i na 4 shafi na 1822. Da kuma Imamut Tirmidhiy acikin sunanu Juzu'i na 5 shafi na 128-128 dukkansu sun ruwaito ta hanyar Abu Juhaifah (Sahabin Annabi sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa: "Na kalli Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) sai naga lallai Alhasan 'dan Aliyu (Radhiyallahu anhuma) yana kama dashi". Hakanan an ruwaito ta hanyar Imamuz Zuhriy daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yana cewa : "BABU