DARAJOJIN AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM)
Wannan shine kashi na hudu acikin bayanin darajoji da falalar iyalan gidan Annabin Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) acikin jerin darussan Zauren Fiqhu :
Sayyiduna Usamah 'dan Zaidu (rta) yace "Watarana na kwankwasa kofar gidan Annabi (saww) akan wasu bukatu, Sai (Naji yana cewa) :
"WADANNAN 'YA'YANA NE, KUMA 'YA'YAN 'DIYATA. YA ALLAH NI INA SONSU KAIMA KASO SU KUMA KASO DUK MAI SONSU".
(Imamut Tirmidhiy ne ya ruwaito).
Imamu Muslim ya fitar da wani hadithi acikin Sahih nasa, juzu'i na 4 shafi na 1822. Da kuma Imamut Tirmidhiy acikin sunanu Juzu'i na 5 shafi na 128-128 dukkansu sun ruwaito ta hanyar Abu Juhaifah (Sahabin Annabi sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa:
"Na kalli Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) sai naga lallai Alhasan 'dan Aliyu (Radhiyallahu anhuma) yana kama dashi".
Hakanan an ruwaito ta hanyar Imamuz Zuhriy daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yana cewa : "BABU WANDA YAFI KAMANNI DA MANZON ALLAH (SAWW) FIYE DA IMAMUL HASAN".
Wata riwayar kuma daga Ma'amar daga Anas bn Malik (rta) yana cewa : "BABU WANDA FUSKARSA TAFI KAMA DA TA ANNABI (SAWW) FIYE DA HASAN BN ALIY BN ABI TALIB (RTA)".
Babban Malamin Tarihin nan Ibnul Atheer ya fa'da acikin littafinsa cewa :
"Abu Ahmadal Askariy yace "Annabi (saww) da kansa ne ya sanya masa suna Al-Hasan, kuma yayi masa "Alkunyah" da Abu Muhammad. Kuma wannan ba'a ta'ba saninsa a zamanin Jahiliyyah ba".
Kuma Ibnul Atheer ya kawo riwayar da ta nuna cewar Ummul Fadhli bintul Harith (rta) wato mahaifiyar su Abdullahi bn Abbas (rta) ita ce ta shayar da Imamul Hasan (ra) da nonon 'danta Qusam bn Abbas (Radhiyallahu anhuma).
Sayyiduna Aliyu 'dan Abu Talib (rta) yace "Yayin da aka haifi Hasan sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yazo yace "KU NUNA MIN 'DAN NAWA. SHIN WANNE SUNA KUKA SANYA MASA?".
Sai nace "Na sanya masa suna "HARBU" (wato Yaqi)".
Sai Manzon Allah (saww) yace "A'A BARI DAI SUNANSA HASAN".
Yayin da aka haifi Alhusain sai muka sanya masa suna "HARBU". Sai ga Manzon Allah (saww) yazo yace "KU NUNA MIN 'DANA..SHIN WANNE SUNA KUKA SANYA MASA?".
Sai nace "Na sanya masa suna "HARBU". Sai Manzon Allah (saww) yace "BARI DAI SUNANSA HUSAINI".
Yayin da aka haifi na ukunsu, sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yazo yace "KU NUNA MIN 'DANA. SHIN WANNE SUNA KUKA SANYA MASA?".
Sai nace "Na sanya masa suna HARBU". Sai Manzon Allah (saww) yace "BARI DAI SUNANSA MUHSIN".
Sannan ya Qara da cewa "NA SANYA MUSU IRIN SUNAYEN 'YA'YAN ANNABI HARUNA NE (AS) WATO SHABAR DA SHUBAIR DA MUSHBIR".
Shi Muhsin daga baya ya rasu tun yana jariri. Kuma bayan shi Nana Fatimah ta haifi 'ya'ya Mata guda biyu da Zainabul Kubra (Ummu Kulthum) da kuma Ruqayyah (amincin Allah da yardarsa sun tabbata garesu).
Anan zamu tsaya da fatan Allah shi Qara mana imani da tsoron Allah, da Tsananin soyayya ga Manzon Allah (saww) da iyalan gidansa tsarkaka.. Ya Allah kayi mana shaidar Son Jikokin Annabinka (saww) ka kiyayemu daga Qiyayyarsu ko Qiyayyar Sahabbansa. Ka sanyamu cikin bayinka masu nagarta don falalarka da rahamarka Ameeen.
AN GABATAR DA KARATUN A ZAUREN FIQHU WHATSAPP RANAR 09/10/2017 19/01/1439).
Comments
Post a Comment