HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (115)
RIKON MARAYU GUDA UKU
****************************
An ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (radhiyallahu anhuma) daga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa :
"DUK WANDA YA RIKE MARAYU GUDA UKU TO (LADANSA) ZAI ZAMANTO KAMAR WANDA YA TSAIWA DARENSA KUMA YA AZUMCI WUNINSA, KUMA YA WUNI YA KWANA TAKOBINSA A ZARE YANA JIHADI ACIKIN TAFARKIN ALLAH, KUMA DANI DASHI ZAMU ZAMANTO TAMKAR 'YAN UWA NE ACIKIN ALJANNAH KAMAR YADDA WADANNAN SUKE 'YAN UWAN JUNA (YANA FA'DAR HAKA SAI YA HA'DA TSAKANIN YATSUNSA GUDA BIYU, BABBAN YATSANSA DA NA KUSA DASHI).
ADUBA :
AT-TARGHEEB WAT-TARHEEB (Juzu'i na 2 shafi na 235).
QARIN BAYANI
***************
Rikon Marayu yana daga cikin ibadu mafiya girman falala a Musulunci. Amma shaitan (La'anatul Lahi alaihi) ya kauda zukatan al'ummah daga kansu saboda sharri in nasa.
Yana da kyau garemu mu rika daukar nauyin marayu wajen ciyarwa da shayarwa ko kuma ilmantar dasu a makarantun Islamiyyah da na boko. Mu rika kulawa da hakkokinsu tare da kishinsu kamar yadda muke yiwa 'ya'yan da muka haifa.
Wannan shine mafi alkhairi fiye da kudaden da muke kashewa wajen yin abubuwan da bazasu amfanemu a lahirarmu ba.
In sha Allahu muna kokarin bude wani asusun taimakon marayu da gajiyayyu, karkashin kulawar Zauren Fiqhu, kuma sunan asusun "ZAUREN FIQHU ISLAMIC FOUNDATION". Kuma shirye-shiryen sunyi nisa. In shaAllah zamu sanar daku da zarar komai ya tabbata.
Allah shi taimakemu ya bamu Qarfin hali da hakurin kula da marayu ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (11/02/2019 06/06/1440).
Comments
Post a Comment