HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (114)
HAKURIN RIKON YARA MATA :
******************************
Hadisi daga Sayyiduna Abu Hurairah (Allah ya yarda dashi) daga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa :
"DUK WANDA YAKE DA 'YA'YA MATA GUDA UKU, KUMA YAYI HAKURI BISA JIBINTAR LAMARINSU, DA BAQIN CIKINSU DA FARIN CIKINSU, ALLAH ZAI SHIGAR DASHI ALJANNAH SABODA JIN QANSA GARESU".
Sai wani mutum yace "Ya Rasulallahi koda guda biyu ne?".
Sai Annabi (saww) yace masa "KODA GUDA BIYU NE".
ADUBA :
AT-TARGHEEB WAT TARHEEB (Juzu'i na 3 shafi na 47).
QARIN BAYANI
***************
Allah madaukakin sarki ya sanya falala mai yawa cikin rikon 'diya mata da tarbiyyarsu fiye da yadda ya sanya acikin rikon 'ya'ya maza. Ba don komai sai saboda irin yadda muhimmancinsu yake acikin al'ummah. Misali :
'Ya mace guda idan ta samu cikakkiyar kulawa tare da tarbiyyah ingantacciya tana iya tarbiyyantar da 'ya'yanta har na makobta har shi kansa Maigidanta tana iya chanza masa wasu muhimman abubuwa a rayuwarsa.
Anan nake jan hankalin iyaye Maza cewa mu dena yin bakin ciki don an haifa mana 'ya'ya mata domin su rahama ne ga mahaifansu ta kowacce fuska mutukar an basu ilimi kuma an kula da tarbiyyarsu.
'Ya'ya Mata sun zarce Maza wajen saukin kai da saukin karbar tarbiyyah da tausayin iyaye. Kuma bincike ya nuna cewa mafiya yawan iyaye sun fi samun kulawa daga 'ya'yansu Mata koda bayan sun tsufa.
Ya Allah ka Qara bamu 'ya'ya masu albarka kuma ka bamu ikon tarbiyyantar dasu bisa tsoron Allah da bin tafarkin Manzonka (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (02/06/1440 07/02/2019).
Comments
Post a Comment