ADDU'AR MU TA YAU

Godiya ta tabbata gareka Ya Allah wanda cikin karamcinka da baiwarka ka sake nuna mana wani Ramadhan din bayan wani..

Ya Allah don tausayinka da jin Qanka ka bamu ikon aikata ayyukan alkhairi ka rabautar damu da samun yardarka matabbaciya. Ka kiyayemu daga sharrin zukatanmu da sharrin shaidan abin jefewa.

Ya Allah ka azurtamu da biyayya gareka acikin wannan watan da bayansa, ka kiyayemu daga sa'ba maka acikinsa da bayansa. Ka sanyamu cikin bayinka wadanda taimakonka da agajinka ke tare dasu a ko yaushe, wadanda tuntube ko kuskure ba zai chutar dasu ba.

Ya Allah ka sanyamu acikin mafiya samun mafi girman rabo daga duk wata rahama da gafara da baiwa da karamci da daukakar daraja, da falala da fifiko da kyauta wacce kake yiwa bayinsa awannan watan, Kuma ka sanyamu cikin jerin farko na bayinka da kake 'yantawa awannan watan.

Ya Allah muna rokonka daga dukkan wani alkhairin da Manzonka kuma bawanka , Annabinmu Muhammadu ya ta'ba rokarka shi. Kuma muna neman tsarinka daga sharrin duk wani abinda Manzonka, bawanka, Kuma Annabinka Muhammadu ya ta'ba neman tsarinka daga gareshi.

Yi salati da aminci adadin yardarka da gudanuwar ikonka, da dawwamar tsarkinka da daukakar mulkinka bisa bawanka Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya da dukkan Salihan bayinka ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (01/09/1440 06/05/2019).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI