FALALAR ADDU'A DA MUHIMMANCINTA (FITOWA TA FARKO)

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI.

SALATI da amincin Allah su tabbata ga zababben Allah, shugabanmu ANNABI MUHAMMADU, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansu yardaddu.

In sha Allahu zamu dora gada wajen da muka tsaya ne acikin maganar FALALAR YIN ADDU'A DA KUMA MUHIMMANCINTA.

Manzon Allah (saww) yace : "HAKIKA ALLAH MADAUKAKIN SARKI RAYAYYE NE, KUMA MAI KARAMCI NE. YANA JIN KUNYAR MUTUM YA CIRA HANNYENSA GARESHI, KUMA ACE YA DAWO DASU TA'BABBU BABU KOMAI AKANSU".

(Sahihul Jaami'i).

Kun ga wannan hadisin yana karantar damu cewa mu rika kyautata tsamaninnu ga Ubangijinmu. Lallai shi yana jin kunyar mu rokeshi bai amsa mana ba.

Awani hadisin kuma Manzon Rahama (saww) yace: "IDAN DAYANKU ZAI YI ADDU'A, KAR YACE "ALLAH GAFARTA MIN IDAN KASO".

LALLAI NE MUTUM YA SANYA MUHIMMANCI CIKIN ROKONSA, KUMA YA GIRMAMA KWADAYINSA, DOMIN SHI ALLAH BABU ABINDA YAFI GIRMAN BMYA BAYAR DASHI".

(Sahihul Jaami'i).

Shi kuma wannan hadisin yana karantar damu kyautata lafazi acikin duk abinda zanu roki Allah.

Sannan Manzon Allah (saww) yace: "BA ZA'A GUSHE ANA AMSA ADDU'AR BAWA BA, MUTUKAR DAI BAI YI ADDU'AR ZUNUBI KO YANKE ZUMUNTA BA. KUMA MUTUKAR BAI YI GAGGAWA BA.

(GAGGAWAR ITA CE) YACE NAYI ADDU'A, NAYI ADDU, AMMA BA'A AMSA MIN BA!.".

DAGA NAN KUMA ZAI YANKE QAUNA YA BAR YIN ADDU'AR.

(Sahihul Jaami'i).

Shi ma dai wannan hadisin yana karantar damu kyautata tsammani ne zuwa ga Ubangijinmu. Mu dena yin mummunar addu'a ko tsinuwa ga mutane..

Acikin hadisi na gaba kuma, Manzo (saww) bai gaya mana wata garabasa mai girma sosai. Yace:

"YAYIN DA AKA KIRA SALLAH, ANA BUDE KOFOFIN SAMMAI, KUMA ANA AMSAR ADDU'A".

(Sahihul Jaami'i).

Shin mutum nawa ne daga cikinmu suke ribatar wannan garabasar akullum sau biyar??.

Kuma Manzon Rahama (saww) ya fada awani hadisin kuma yana cewa "ADDU'A GUDA BIYU BA'A MAYARWA:
1. ADDU'A YAYIN KIRAN SALLAH.
2. ADDU'A ALOKACIN YAQI. YAYIN DA SUKE YIWA JUNANSU RAUNI".

(Sahihul Jaami'i).

Awani hadisin kuma wanda Bukhari, Muslim sun ruwaitoshi, Manzon Allah (saww) yace: "AMMA ITA SUJJADA, KUYI KOKARIN WAJEN ADDU'A CIKINTA. DOMIN KUNA KUSA DA A AMSA MUKU".

Hadisi na gaba kuma zai zo mana da fa'idah mai girma. Manzon Allah (saww) yace: "DUK WANDA YA FARKA CIKIN DARE, KUMA YAYIN FARKAWARSA YACE:

LA ILAHA ILLLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, YUHYEE WA YUMEETU, BIYADIHIL KHAIRU WA HUWA 'ALA KULLI SHAY'IN QADEER. SUBHANALLAHI WAL-HAMDU LILLAHI, WALA ILAHA ILLLAL LAHU, WALLAHU AKBAR. WALA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH.

Sannan yace : "YA ALLAH KA GAFARTA MIN" KO KUMA YA YI WATA ADDU'AR, ZA'A AMSA MASA.

IDAN KUMA YA TASHI YAYI ALWALA YAYI SALLAH, TO ZA'A KARBI SALLAR TASA".

(Sahihul Jaami'i).

Wannan falala ce mai girma tare da garabasa wacce kowa zai iya kokarinsa domin samun dacewa acikinta. Maza da mata, yara da manya duk zasu iya cin wannan moriyar.

Mun gabatar da wannan karatun ne acikin ZAUREN FIQHU WHATSAPP 1,2,3, da 4. Da fatan Allah shi amfanar damu da abinda muka karanta.

SALLU ALAN NABIYYI WA AHLI BAITIHI WA SAHBIH.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.  07064213990 (05/05/2017).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI