MAI MATSAYIN QUREWA (SAWW).

Manzon Allah (saww) shine cikakken Malamin al'ummah. Malamin da bai koyi karatu awajen kowa ba, amma awajensa kowa yake kwankwadar ilimi.

Acikin maganganunsa zaka samu Ilimai na zahiri da na 'boye. Zaka ji Ilimin Geography, Physiology, Astrology, Gynaecology, Botany, Economy, da sauran dubban ilimai wadanda babu wani 'Dan Adam da ya sansu.

Allah ya fifita Annabi Aadamu akan Mala'iku ne tunda ya san ilimin Sunaye wanda su basu sani ba.. Don haka Allah yace suyi masa Sujadah su gaisheshi.

Shi kuwa Annabi Yusufu (as) Allah ya fifitashi akan sauran 'Yan uwansa ne da ilimin sanin fassarar Mafarkai da kuma Mafita acikin al'amura boyayyu. Don haka Allah ya bashi Mulki da fifiko asamansu.

Shi kuwa Khidru (as) Allah ya sanar dashi wani ilimi ne tsakaninsa dashi, ba tare da wani atsakani ba.. Ya sanar dashi Ilimin hangen nesa. Don haka ma ya bashi Manyan Annabawa suka zama Almajiransa. Wato irin su Annabi Musa da Yusha'u (alaihimus Salam).

Annabi Dawud Allah ya sanar dashi ilimin sanin Qarafa da makamashi da kayan yaqi. Don haka Allah ya bashi Mulki kuma ya Hore masa tsuntsaye da duwatsu suke yin tasbeehi da zikirin Allah tare dashi.

Annabi Sulaiman (as) Allah ya bashi Ilimin sanin Maganar Tsuntsaye da dabbobi, Don haka Allah ya hore masa Iska ta zama abin hawansa, da kuma Shaitanun Aljanu masu taurin kai suna hidima agareshi.

Annabi Eesa (as) Allah ya bashi Ilimin sani Attaura da Injeela don haka Allah ya azurtashi da sunansa mafi girma wanda dashi yake kiransa ya rayar da matattu, ya bude ikon makafi, ya warkas da guragu da mahaukata.

Shi kuwa Annabina Shugabana, Macecina, Majinginan lamarina (saww) Allah ya sanar dashi Ilimin farko da na Qarshe, sannan ya Qara masa da ilimin sanin Shari'a da hukunce Hukunce, da kuma Ilimin gyaran Zukata. Don haka Allah yayi masa baiwar da tafi ta dukkan Annabawa (as).

Idan Mala'iku sunyi ma Annabi Aadam Sujadah sau 'daya, to shi kuma Annabi Muhammadu (saww) Salati suke yi masa babu tsayawa babu denawa.

* Idan Annabi Yusufu ya samu Mulki da daukakar sarauta saboda iliminsa na fassarar Mafarkai, to shi kuwa Annabi Muhammadu (saww) ya Jagoranci dukkan Annabawa da Manzanni yayi musu sallah, Sannan yayi wa Mala'iku ma.

Idan Khidru ya san Ilimin Hangen nesa, to shi kuwa Annabi Muhammadu (saww) shi ke bada labarin abubuwan da zasu faru aranar Alqiyamah. (Qarshen Matsayi kenan).

Idan Annabi Dawud da Annani Sulaiman sun samu Horewar Iska da duwatsu da Aljanu, shi kuwa Annabi Muhammadu (saww) Mala'iku ne suke hidimta masa har suna tayashi Yaqi.

Idan Annabi Eesa (as) yana raya matattu, ya warkas  da guragu da makafi, to shi kuwa Annabi Muhammadu (saww) Makaho yayi Tawassuli dashi ya warke. Gurguwa ta ganshi amafarki ta samu waraka afili. Sunanshi yana nan ajikin kowanne rayayye acikin halittu.

Ya raya duwatsu da izinin Allah sunyi magana dashi, Ya raya kutturen dabino anan duniya da izinin Allah kuma ya dasashi acikin Aljannah.

Shine kadai Annabin da ya taba zuwa Sidratul Muntaha, Kuma ya hau saman Al'arshi da takalminsa.

Duk da Mulkin Annabi Sulaimanu (as) bai ta'ba Damke shaitan ba, Kuma shaitanu aka hore masa amma basuyi imani dashi ba..

Ya Allah yi salati da tasleemi ga Ma'abocin Matsayin Qurewa da Muqamin abin yabo da Tutar godiya. Albarkacin wannan salatin ka tabbatar damu bisa sunnarsa, Ka sadar damu dashi aduniya da lahira. Ka sanya Zauren Fiqhu ya zamanto dalilin shigarmu zuwa ga dausayin Aljannar Fidausi acikin Makobtakar Fiyayyen Abin Qauna (saww).

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1) 07064213990 05/04/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI