ALBARKAR TAFIN HANNUNSA (ﷺ)

Yana daga cikin Mu'ujizozin Manzon Allah (saww) Allah yakan sanar dashi boyayyun abubuwan da suka faru a baya, ko kuma wadanda zasu faru nan gaba. Kuma in dai ya fadi abu da bakinsa mai albarka, to lallai sai abun ya faru kamar yadda yace. 

Hakanan idan ya dora hannunsa akan abu, sai abun yayi albarka ko menene. Idan kuma akan Majinyaci ne sai jinyar ta bar jikinsa cikin yardar Allah. 

Akwai wani Sahabi mai suna Sayyiduna Abdullahi bn Busrin (ra) yana da wani ciwo akan fuskarsa wanda ya sanya fuskar tasa tayi baqi. 

Watarana Manzon Allah (saww) ya dora hannunsa akansa, sai yace ma jama'a:

"WANNAN YARON ZAI RAYU TSAWON QARNI GUDA (WATO SHEKARA 100)".

"KUMA KAFIN YA RASU SAI WANNAN CIWON YA BAR FUSKARSA".

Hakan kuwa akayi. Sayyiduna Abdullahi bn Busrin sai da ya rayu tsawon shekara 'dari aduniya. Kuma wannan ciwon ya rabu da fuskarsa. Hasali ma shi yana daga cikin manyan Khadiman Manzon Allah (saww). Shi yake daukar Akushin nan na Manzon Allah (saww) mai suna "Garra'u" duk inda za'a je. 

- Imamul Hakim ne ya ruwaito hadisin tare da Abu Nu'aym da Baihaqiy. 

Ya Allah ka yarda muso Annabinka (saww) ka hore mana biyayya gareshi da koyi da halayensa. Ameeen. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (26-04-1438  24-01-2017).

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI