LABARIN UMMU MALIK (RTA)


Akwai Wata Mata mai suna Ummu Malik ta kasance tana hidimta ma Manzon Allah (saww).

Watarana ta zuba Man girki acikin Salka sannan ta tafi dashi ta kai masa (saww).

To rannan ta wayi gari batta da Man gyadan ya Qare. Kuma gashi 'Ya'yanta suna bukatarsa zasu ci abinci. Da taje ta dauko Salkar sai ta tarar da ita acike Fal da man gyada.

Ta dauko ta bama yaranta suka ci abinci dashi.. Ta kasance duk lokacin da take bukatar Mai agidanta, da ta dauko salkar sai ta tarar da ita acike Gal da mai.

Rannan kawai sai ta juye man, ta tatse Salkar gaba daya... Tun daga ranar sai ta deba ganin Komai acikin salkar. Don haka taje ta sanar da Manzon Allah (saww).

Sai yace mata : "DA ACHE BAKI TATSESHI BA, DA SAI YA ISHEKI HAR TSAWON RAYUWARKI".

Acikin wata ruwayar kuma ance da ta koma gida sai taga Salkar man gyadar kamar ba'a juye ba.  Don haka sai hankalinta ya tashi. Ta dawo wajen  Manzon Allah (saww) Tace masa "Ya Rasulallahi ko an saukar da wata ayah. e game dani?".

Sai ya tambayeta "MENENE YA FARU YA UMMA MALIK?" Sai tace "Mai yasa ka mayar min da kyautata wacce na kawo".

Ds Annabi (saww) yaji haka sai ya kira Bilaalu ya tambayeshi akan haka. Sai Bilaalu yace "Na Rantse da Girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, Na juye Man gyadan,  na tatse Salkar har sai da naji kunya".

Sai Annabi (saww) yace mata "MURNA TA TABBATA GAREKI YA KE UMMU MALIK!. HAKIKA ALLAH NE YA GAGGAUTO MIKI DA LADAN ABINDA KIKAYI".

ADUBA :

# MU'UJAMUL KABEER (25/146).
# DALA'ILUN NUBUWWAH (559).
MAJMA'UZ ZAWA'ID (Juzu'i na 8 shafi na 309).

ZAUREN FIQHU : Hakika wannan kadan ne daga cikin Karamomin da Allah yake girmama Waliyyansa. Hakika mu mun yarda cewar dukkan Sahabban Annabi (saww) Muminai ne, adalai ne, kuma Salihan bayin Allah ne. Sun hidimta ma Annabi (saww). Don haka Allah ya girmamasu ya basu karamomi daban daban.

Musamman Manyan cikinsu irin su Sayyiduna Abubakrin da Umar da Uthmanu da Aliyu da sauransu. Allah ya yarda dasu baki dayansu. Su ma sun yarda dashi.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (11-01-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI