GWARZON MUSULUNCI SALMANUL FARISIY (RA)
Sayyiduna Salmanul Farisy shine Sahabin da yafi dukkan Sahabbai yawan shekaru aduniya. Domin kuwa yafi shekara 100 yana jiran Zuwan Manzon Allah (saww).
Wasu daga cikin Malaman tarihi sunce Shekara 170 ya ayu aduniya. Amma wasu kuma Sunce ya haura shekaru 300 ma yana raye.
Watakil wadanda suka ce ya haura shekara 300 din zancensu yana da Qarfi domin kuwa Salmanul Farisy ya zauna awajen Manyan Malaman addinin Kirista masu yawa.
Lokacin da ya gudo daga garinsu ya taho garin Shaam (Syria) sai ya tambayi mutanen garin cewa su nuna masa Babban Malamin addinin Nasaara (Kiristanci) Saboda alokacin nan musulunci bai bayyana ba.
Sai suka nuna masa babban Paada (Bishop) na garin. Yaje ya zauna tare dashi tsawon shekaru, har mutumin nan ya tsufa basu rabu ba. har zuwa lokacin da Paadan nan ya rasu.
Bayan ya rasu, Sai aka nada magajinsa. Sai Salmanul Farisy ya zauna tare da wannan magajin nasa tsawon shekaru har shima yazo rasuwa.
Da yazo rasuwa sai Sayyiduna Salmanu ya tambayeshi shin Yanzu adoron Qasa a ina zan samu wani mutumin kirki wanda yake kan addinin nan namu? "
Sai wannan Paadan ya gaya masa Sunan wani mutum awani gari. Salman Alfarisy ya tafi wajensa ya zauna tsawon shekaru masu yawa. Shima da zai rasu sai Salmanu yayi masa irin waccan tambayar.
Don haka ya nusar dashi zuwa ga wani Paadan. Da haka-da haka dai Salmanul Farisy ya zauna awajen Manyan Malaman addinin Kirista kamar guda biyar. Awata ruwayar kuma ance awajen mutum bakwai ya zauna.
Har zuwa lokacin da Malaminsa na karshe yace masa : "Yanzu adoron Qasa babu sauran wani mutum guda wanda yake kan gaskiya cikin addinin nan namu. Amma kuma mun shigo daidai lokacin bayyanar Annabin Qarshen Zamani. don haka kaje ka nemeshi ka gaskatashi ka yi imani dashi"
Sai Salmanul Farisy ya tambayeshi "Shin ko akwai wasu alamomi wadanda dasu zan gane Wannan Annabi? "
Sai Malamin nasa ya gaya masa alamomin kamar haka:
1. Alamarsa ta farko ita ce wannan Annabin Qarshen ba ya cin sadaka.
2. alama ta biyu kuma yana cin kyauta.
3. alama ta uku kuma, Akwai Khatimin Annabta abayan kafadarsa. .
Daga nan yaci gaba da zama yana kasuwanci har yatara dukiya da dabbobi masu yawan gaske. har lokacin da ya samu wasu ayarin 'Yan kasuwa, ya basu dukkan abinda ya mallaka, Don kawai su kawoshi yaga Manzon Allah (saww).
Anan zamu tsaya sai gobe kuma insha Allah.
DAGA ZAUREN FIQHU
Comments
Post a Comment