CIKIN QABARIN MUMINI
Ranar da aka sanya Mumini cikin Qabarinsa, rana ce mafi Muhimmanci gareshi. Rana ce wacce zai fita daga gidan wahala da Qunci da bakin ciki (wato duniya). Zai koma zuwa ga gidan hutu da yalwa da farin ciki. Rana ce wacce Mumini zai fara girbar alkhairin da ya shuka.. Wato sallolinsa da azuminsa da sadakokinsa da Zikiransa wadanda ya gabatar. Rana ce wacce Ubangijinsa zai cika masa alkawarin da yayi masa.. Wato Alkawarin cewa zai, shigar dashi cikin ni'imarsa mutukar dai yayi imani kuma ya aikata ayyuka na Kwarai. Rana ce wacce zai rabu da danginsa da iyalansa da dukiyoyinsa, Zai shiga cikin Ni'imar Ubangijinsa, da kuma arzikin da ba ya Qarewa. Rana ce wacce Mumini zai chiza yatsansa, yana burin inama za'a bashi damar dawowa duniya domin ya aikata wasu Qarin ayyukan alkhairi. Saboda irin girmamawar da ya samu awajen Ubangijinsa. Rana ce wacce dukkan 'Yan uwansa da danginsa suna cikin Kuka, da Bakin ciki. Amma shi kuwa yana cikin farin ciki da annashuwa. Wasu daga