CIKIN QABARIN MUMINI


Ranar da aka sanya Mumini cikin Qabarinsa, rana ce mafi Muhimmanci gareshi.

Rana ce wacce zai fita daga gidan wahala da Qunci da bakin ciki (wato duniya). Zai koma zuwa ga gidan hutu da yalwa da farin ciki.

Rana ce wacce Mumini zai fara girbar alkhairin da ya shuka.. Wato sallolinsa da azuminsa da sadakokinsa da Zikiransa wadanda ya gabatar.

Rana ce wacce Ubangijinsa zai cika masa alkawarin da yayi masa.. Wato Alkawarin cewa zai, shigar dashi cikin ni'imarsa mutukar dai yayi imani kuma ya aikata ayyuka na Kwarai.

Rana ce wacce zai rabu da danginsa da iyalansa da dukiyoyinsa, Zai shiga cikin Ni'imar Ubangijinsa, da kuma arzikin da ba ya Qarewa.

Rana ce wacce Mumini zai chiza yatsansa, yana burin inama za'a bashi damar dawowa duniya domin ya aikata wasu Qarin ayyukan alkhairi. Saboda irin girmamawar da ya samu awajen Ubangijinsa.

Rana ce wacce dukkan 'Yan uwansa da danginsa suna cikin Kuka, da Bakin ciki. Amma shi kuwa yana cikin farin ciki da annashuwa.

Wasu daga cikin Muminai ba za'ayi musu tambayar Qabari ba. Wasu kuwa za'a yi musu. Sai dai za'a rangwanta musu kuma za'a saukaka musu hanyoyin mayar da jawabi ga Mala'ikun Qabarin.

Bayan Mala'ikun sun kammala yi masa tambaya kuma ya basu amsa, Su zasu fara yi masa albishir na samun matsayi kyakkyawa awajen Allah.

Za'a fadada masa Qabarinsa kamar nisan iyakar ganinsa, za'a haskaka masa a ni'imta masa. Har sai ya zama wani dausayi ne daga dausayoyin aljannah.

Za'a bude masa Qofofin alkhairi wato zai rika kallo zuwa ga Masaukinsa na din-din-din acikin Aljannah.

Ya Allah kasa muna da rabo.  Ya Allah muna rokonka aljannarka kuma muna neman tsarinka daga Azabar wuta.

Salati da aminci su tabbata ga Annabin da yazo da Qur'ani acikin watan Ramadhan, tare da iyalan gidansa da Sahabbansa baki daya.

An gabatar da karatun nan ne a Zauren Fiqhu Whatsapp -3 ranar 31-05-2016.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI