BASU SON 'YARSU TA AURI TALAKA

TAMBAYA TA 1928
********************
Assalamullahi alaika, Allah y qara lpy d rayuwa mai ampani. amin. mallam dan Allah ataimaka mun da addu'ar dazan dunga yi. Mun kasance muna son juna d saurayina, kuma aure ya kawoshi. Amma wadanda nake zaune awajensu basa so wai saboda malamin makaranta ne har sukancemin wai "me nasama yaci bare yaba naqasa"
Ni kuma nafi son yin auren kwanciyar hankali da ganin mutuncin juna koda kullum sai ya fita zai samo.

Dan Allah mallam ataimaka mun da addu'ar dazan keyi kan Allah ya Fahimtar dasu su goya mun baya.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Abinda zakiyi da farko shine Ki dogara ga Allah, domin duk wanda ya dogara ga Allah sai Allah din ya isar masa akan dukkan damuwarsa.

Ki yawaita yin addu'ar nan ta Annabi Yunus (as) wacce Manzon Allah (saww) yace "BABU WANI WANDA YAKE CIKIN BAKIN CIKI DA ZAI KARANTA-TA FACHE SAI ALLAH YA YAYE MASA".

Addu'ar ita ce "LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZWALIMEEN".

Ki rika yinta acikin Sujadarki da sauran guraben da Allah yafi amsar addu'a.

Ki yawaita Salati da tasleemi bisa Manzon Rahama (saww) domin kuwa yawaita salati agareshi yana daga cikin mafiya girman hanyoyin samun biyan bukatu da yayewar damuwa.

Daga karshe ina jan hankali ga iyaye masu irin wannan mummunan ra'ayin cewa Kuji TSORON ALLAH Ku gyara halayenku. Qarancin sanin Allah ne yasa kuke ganin kamar idan yarinyarku bata auri mai dukiya ba, wai ba zata samu rayuwa mai kyau ba..

Irin wannan ra'ayin Yahudawa ne, wadanda sukayi ma Allah tawaye. Kuma duk auren da aka ginashi bisa Tinkaho da dukiya ko arzikin duniya, BA ZAI YI ALBARKA AWAJEN ALLAH BA!

Dukkan iyaye Musulmai na kirki suna gina auren 'ya'yansu ne bisa Kyakkyawar niyyar raya sunnar Manzon Allah (saww). Kuma addini da tarbiyyah suke kallo ba wai yawan dukiya, ko girman albashi, ko alfaharin duniya ba.

Idan mutumin da kuka yarda da rikon addininsa yazo neman aure gareku to lallai ku aurar masa. Idan bakuyi haka ba kuma, to fitina zata afku adoron Qasa tare da 'barna mai girma.

Ku sani cewa Allah ne ke bada arziki. Kuma yana da ikon talautat da mai arziki, kuma ya azurta Matalauci. Shi keda ikon juya al'amuran bayinsa yadda yaso.

Allah shi kiyayemu.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (10-05-2016)

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI