HUKUNCIN MASU SAIDA SIGARI DA KAYAN MAYE
TAMBAYA TA 1934
********************
ASSALAMU ALAIKUM MAL DON GIRMAN ALLAH A'ANSA MIN TAMBAYA. YAYA HUKUNCI MAI SAYAR DA SIGARI DA KWAYOYIN SA MAYE A MUSULINCI?
NAGODE ALLAH YAKA DA ALHERI AMIN DAGA DALIBINKA SHAFIU BELLO ANKA ZAMF WASSALAM
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Duk abinda amfani dashi ya zama Haramun, to hakanan sayar dashi ko dakonsa ko shukawa, ko girbewa ko sarrafawa duk HARAMUN ne.
Kuma dukkan abinda ke sanya maye, sunansa giya ne. Kuma Allah ya haramta giya, ya kuma tsine ma masu yinta da masu dakonta da masu shayar da ita da masu sayar da ita.
Ita kuwa Sigari kayan Almubazzaranci ce. Kuma Allah yace su Amubazzarai 'Yan uwan shaitan ne. Shi kuwa shaitan ya butulce ma Ubangijinsa ne.
Hukuncin mai sayar da irin wadannan abubuwan shine ya aikata HARAM. Domin kuwa Allah yace "KUYI TAIMAKEKENIYA BISA BIN ALLAH DA KUMA TAQWA. KADA KUYI TAIMAKEKENIYA CIKIN SA'BON ALLAH DA QETARE IYAKOKINSA".
Sayar da Sigari da kayan maye kamar taimakawa ne wajen sa'bon Allah. Don haka bai halatta ba.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (14-05-2016).
Assalamu Alaikum Dan Allah inaso a fada min yanda zan tura tambayoyi na a wannan Zauren
ReplyDeleteAssalama alaikum dan allah ina so a gayamin yadda zan iya tura tambaya akan wannan shafin
ReplyDelete