HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (043)

CIKAWA DA KYAKKYAWAN AIKI
**********************************
Hadisi daga Huzaifah Ibnul Yamaan (rta) yace : "Na shiga wajen Manzon Allah (saww) alokacin jinyarsa wacce ya rasu acikinta. Sai yace "ZAUNAR DANI".

Sai Sayyiduna Aliyu (ra) ya zaunar dashi ya jinginar dashi zuwa ga Qirjinsa.

Sai nace ma Aliyu din "Ya Abu Hamza, Ka kwana kana jinyarsa (wato ina so nima ka barni inyi jinyar Manzon Allah).

Sai Manzon Allah (saww) yace: "YA KAI HUZAIFAH, AI ALIYU YAFI KA CHANCHANTA DA WANNAN AIKIN..  MATSO NAN KUSA DANI".

(Da na Matso kusa dashi sai yace). "YA HUZAIFAH! DUK WANDA "LA ILAHA ILLAL LAAHU" TA ZAMANTO AIKINSA NA KARSHE KAFIN MUTUWARSA, TO ZAI SHIGA ALJANNAH. KO KUMA ZA'A GAFARTA MASA.

"YA HUZAIFAH! DUK WANDA AKA CIKA MASA (AIKINSA NA KARSHE) KAFIN MUTUWARSA DA AZUMIN RANA GUDA DOMIN NEMAN YARDAR ALLAH, ZAI, SHIGA ALJANNAH, KO KUMA ZA'A GAFARTA MASA".

"YA HUZAIFAH! DUK WANDA AKA CIKA MASA AIKINSA NA KARSHE KAFIN MUTUWARSA, DA CIYAR DA MISKINI GUDA DON NEMAN YARDAR ALLAH, ZA'A GAFARTA MASA, KO KUMA ZAI SHIGA ALJANNAH".

Sai Huzaifah yace "Ya Rasulallahi, Shin in 'boye wannan albishir din kp kuwa in bayyanar dashi?". Sai yace ''A'A KA BAYYANAR DASHI".

ADUBA :

- Musnadul Harith (Zawa'idul Haithamiy) Juzu'i na 1 shafi na 360.

BAYANI
********
Wannan hadithin yana karantar damu abubuwa da yawa. Daga ciki akwai :

1. FALALAR KALMAR SHAHADA : Ita ce fiyayyen abinda dukkan Annabawan Allah (as) suka fa'da da harshensu. Kuma babu masu samun babban rabo aranar lahira fiye da "AHLU LA ILAHA ILLAL LAAH" (Wato mafiya yawan fadarta aduniya).

Ita katangar Allah ce. duk wanda ya shiga cikinta to ya tsira daga dukkan azaba.

Duk wanda yake yawaita yinta, to koda Mutuwa ce tazo masa in sha Allahu ba zai kasa fadarta ba.

2. FALALAR YIN AZUMI : Lallai Azumi garkuwa ne daga dukkan Qunci. Kuma hanya ce ta samun tsarkakewar Ruhi da kuma kusanci da Allah da samun Gafararsa. Duk wanda Azumi ya zama shine aikinsa na karshe, to zai samu gafarar Allah da kuma Aljannarsa.

3. FALALAR CIYARWA : Ciyar da Miskinai domin Allah, yana daga cikin manyan hanyoyin gusar da fushin Allah, da samun kulawarsa. Yana da kyau mu rika taimaka ma Almajirai da Miskinai, da Nakasassu da sauran masu Qaramin Qarfi.

4. YAWAITA AYYUKAN ALKHAIRI : Ko yaushe ka zama mai kokarin bin Allah da neman yardarsa. Kar ka kasance cikin masu gangancin saɓa masa. Domin baka san shin wanne aiki ne zai zama aikinka na ƙarshe ba.Baka san yaushe ne zaka rasu ba.

Allah yasa mu dace.

DAGA ZAUREN FIƘHU (09-SHAWWAL 1437) 16-05-2016.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI