WACECE NANA FATIMAH?
AN HAIFI S AYYIDAH FATIMAH (A.S) acikin garin Makkah, ranar 20 ga watan Jumaada akhir, ashekara ta biyar bayan Manzanci. Wato shekara 8 kafin hijra. (kamar yadda yazo acikin "SIYARU A'ALAMIN-NUBALA'I. Ta taso cikin kyakkyawar tarbiyyah wacce babu kamarta. Kasancewar Mahaifiyarta ita ce Nana Khadeejah bintu Khuwailid (rta) wacce ta zamto Mafificiya acikin Matayen Zamanin da, harma na yanzu. Mahaifinta kuwa shine Shugaban dukkan Annabawa da Manzanni (saww). Kuma shine mafificin halittu ta wajen kyawun hali da dabi'u. Nana Fatimah fara ce kyakkyawa mai kyawun diri. Tafi kowa daukar kamannin mahaifinta. Tayi kama dashi wajen zamansa da tashinsa da tafiyarsa da maganarsa da murmushinsa. Nana Fatimah ta taso da kaifin hankali da basira wacce ta zarce sauran tsararrakinta. Don babu tamkarta acikin Matayen zamaninta. Ta kasance tana taimakon mahaifinta wajen isar da sakon Allah, Kuma duk da kasancewarta yarinya Qarama alokacin, takan nuna fushinta akan abinda kafirai suk