FIQHUN AZUMI DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (13)

FIQHUN AZUMI DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (13)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Allah kayi salati irin naka abisa Shugaban Manzanninka, kuma Jagoran Halittunka, Annabinmu Muhammadu tare da Iyalan gidansa Tsarkaka da Sahabbansa Madaukaka.

Awancan karatunmu wanda ya gabata, munyi magana akan abubuwan da suke Karya azumi amma bangaren wadanda suke wajabta ramuko ba tare da kaffara ba.

Yanzu kumq insha Allahu zamu shiga bangaren wadanda suke karya Azumi kuma suke wajabta Ramuko da kuma Kaffara gaba daya.

★ JIMA'I shine abinda yake warware azumi, kuma yake wajabta Qadha'i  tare da kaffarah.

Saboda hadisin da Bukhary da Muslim da Abu Dawud da Ahmad da Tirmizy suka ruwaito daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra):

"Wani mutum yazo wajen Manzon Allah (saww) sai yace masa:

"YA RASULALLAHI NA HALLAKA!!"

Sai Annabi (saww) yace masa "MENENE YA HALLAKAR DAKAI?".

Sai yace "Na afkawa Matata acikin Ramadhana!!".

Sai Manzon Allah (saww) yace masa "SHIN KANA DA KUYANGAR DA ZAKA 'YANTA?"

Sai yace "A'a".

Sai Manzon Allah (saww) yace masa "SHIN ZAKA IYA YIN AZUMIN WATA BIYU AJERE?".

Sai yace "A'A".

Sai ya sake ce masa "TO SHIN KANA DA ABINDA ZAKA CIYAR DA MISKINAI SITTIN?"

Sai yace "A'a'.

Sai ya samu waje ya zauna.

Sai aka kawo ma Manzon Allah (saww) wani buhu da dabino acikinsa. Sai yace ma wannan mutumin "JEKA KAYI SADAQA DA WANNAN".

Sai mutumin yace "Shin zanyi sadakar ne abisa wadanda suka fimu talauci?"

"Ai atsakanin bakaken duwatsun nan guda biyu babu mutanen wani gida wanda suka fimu talauci, ko kuma bukatuwa izuwa wannan dabinon".

Sai Annabi (saww) yayi murmushi har sai da kyawawan hakoransa suka bayyana. Sannan yace masa: "DAUKI KAJE KA CIYAR DA IYALINKA DASHI".

Mafiya yawan Malamai Ma'abota ilimi sun tafi akan Wajibcin yin kaffarar abisa Mata da miji mutukar dai dukkansu sunyi Jima'in ne da gangan, Kuma ba tilastasu akayi ba, da rana acikin watan Ramadhana bayan sun riga sun dauki niyyar azumi.

Malamqn sunce idan sunyi ne da Mantuwa, ko kuma tilastasu akayi, ko kuma dama chan basu dauki niyyar azumin ba, to babu kaffara akan kowanne daga cikinsu.

Idan kuma shi Mijin ne ya matsa ma matarsa har sai da ya afka gareta, to babu kaffara akanta. Sai dai ramuko kawai zatayi.

Shi kuwa sai yayi ramuko tare da kaffara gaba daya.

★ Amma shi Imam Shafi'iy (rah) yana ganin cewa babu kaffara akan ita matar ko tilasta mata akayi, ko kuma abisa son ranta ne. Ramuko kawai zatayi.

An ruwaito irin wannan fatawar daga wajen Imamu Ahmad bn Hanbal shima.

Shi kuwa Imam Abu Haneefah (rah) yana ganin cewa CIN ABINCI DA GANGAN, KO KUMA AMFANI DA WANI MAGANI WANDA ZAI AMFANAR DA JIKIN DAN ADAM, DA GANGAN BA TARE DA MANTUWA BA,  YIN HAKA YANA WAJABTA KAFFARA DA RAMUKO BAKI DAYA.

Su kuwa Mazhabin Imamu Malik (rah) sunce "KAFFARA TANA WAJABTA AKAN DUK WANDA YA KARYA AZUMINSA TA HANYAR DUK ABUBUWAN DA MUKA LISSAFA ACHAN BAYA, (su jima'i, istimna'i, cin abinci da gangan).

Sai dai kawai Fitar maniyyi wanda ya fito ba da gangan ba, kuma ba ta dalilin motsawar sha'awa ko kallo ba.

Sunce shi wannan ba ya wajabta kaffara. Hakanan Fitar Maziyyi ma ba ya wajabta kaffara sai dai ramuko idan an fiddashi ne da gangan ta hanyar wasanni ko kallo ko tunanin da ya shafi Jima'i.

★ MALIKIYYAH SUN AJIYE WASU SHARUDA WADANDA SAI SUN CIKA SANNAN AZUMIN YAKE ZAMA SAI ANYI KAFFARARSA. GA SHARUDAN KAMAR HAKA:

1. Idan ya kasance an karya azumin ne acikin shi kansa watan Ramadhana.

Amma idan ya kasance awani azumin ne daban, kamar na Ramuko ko Azumin bakance, ko na Tadawwu'i ko na kaffara, to kaffara  bata wajabta akan wanda ya karya azumin ba (koda ta hanyar jima'i ko cin abinci  ne) Sai dai zai yi Ramuko ne kawai.

2. Idan ya kasance da gangan aka karya azumin, to wajibi ne ayi kaffara.

Amma idan ta hanyar Mantuwa ne ko kuskure ko kuma wani uzuri kamar Rashin lafiya, to babu kaffara. Ramuko kawai za'ayi.

3. Idan ya kasance mutum ya karya azumin ne abisa za'bin kansa ba tilastashi akayi ba, to zai yi kaffara da ramuko.

Amma idan tilasta masa akayi, to babu kaffara akansa sai dai ramuko.

4. NA HUDU: Idan ya kasance wanda ya karya azumin yana sane da haramcin wannan abun, to wajibi ne yayi kaffara da ramuko.

Amma idan bai san cewa haramun bane, misali kamar wanda bai dade da shiga musulunci ba, watakil shi azatonsa cin abinci ne kawai haram, sai yaje ya afkawa iyalinsa abisa zatonsa cewa yin hakan bai haramta ba, to wannan ramuko ne kawai akansa. Amma babu kaffara.

Rashin sanin cewa yin hakan yana wajabta kaffara, ba zai amfaneshi ba. Mutukar dai yasan da haramcin abun.

5. NA BIYAR: Idan ya kasance wanda ya karya azumin bai kiyayewa ne da alfarmar watan, kuma babu wani tawili na kusa acikin dalilan karya azumin nasa, to wajibi ne zai yi kaffara.

Amma idan ya kasance yana da wani taweeli acikin dalilansa, to kaffara bata wajabta akansa ba. Misali:

A.) Wanda ya karya azuminsa ta hanyar tilasta masa da akayi, ko kuma ta dalilin mantuwar da yayi, sai kuma yaci gaba da cin abinci, bai san cewa Wajibi ne ya kama bakinsa har zuwa faduwar rana ba, to wannan babu kaffara akansa.

Domin kuwa yana da taweeli akusa dashi. Taweelin kuwa shine rashin sanin wajibcin kame bakinsa.

B.) Wanda yayi tafiyar da bata kai ayi mata Qasaru ba, amma sai yaci gaba da cin abincinsa abisa zaton cewar tafiyar tasa takai yadda za'a ajiye azumi.

To shima wannan babu kaffara akansa saboda yana da taweeli acikin dalilansa.

C.) Wanda yaga watan shawwal (watan Qaramar sallah) aranar talatin ga Ramadhan, kuma alokacin nan rana bata fadi ba, sai yaje yaci abincinsa abisa zaton cewa hakan ya halatta gareshi, watakil ya dogara da hadisin da Manzon Allah (saww) yake cewa:

"KUYI AZUMI SABODA GANINSA (WATO GANIN WATAN), KUMA KU AJIYE AZUMI SABODA GANINSA"

To shima wannan babu kaffara akansa.

★ Amma akwai wadanda shari'a batta karbar Uzurinsu saboda taweelinsu manisanci ne. Misali:

# Kamar mutumin da yake marara lafiya, abisa al'ada kullum sai zazzabi mai zafi ya rufeshi, sai ya wayi gari ba ya azumi saboda tsammanin zuwan zazzabin nan, to shi wannan Uzurinsa ba karbabbe bane.

Kaffara ta hau kansa. Koda ace zuwa jimawa kadan zazzabin ya rufeshi, duk da haka kaffarar tana kansa.

# Matar da take zaton cewar ai gobe hailarta zata zo, sai taki daukar niyyar azumi, ta wayi gari babu azumi saboda tsammanin zuwa haila, to itama kaffata ta hau kanta.

Ko da kuwa hailar tazo mata daga baya.

6. ABU NA SHIDA: idan ya kasance abinda aka karya azumin dashi an sanyashi ya shiga ne ta baki, to akwai kaffara.

Amma idan abun an sanyashi ya shiga ne ta kunne ko ta ido, Ramuko za'ayi amma babu kaffara.

7. NA BAKWAI KUMA NA QARSHE SHINE: Idan ya kasance abun ya sadu izuwa uwar-hanji, ko za'ayi kaffara.

Amma idan ya kasance an dawo da abun bayan yaje har  makogoro, to babu komai akansa (babu kaffara, ko Ramuko).

# Wadannan abubuwan da muka zayyano tun daga karatunmu na rannan har zuwa karatunmu na yau, shine abinda Malaman Fiqhu sukayi bayaninsa cikin abubuwan da suke karya azumi.

Tun daga wadanda suke wajabta ramuko kadai, har zuwa wadanda suke wajabta ramuko tare da kaffara.

Malamai sunce mafi Inganci acikin maganganun baki daya, shine abinda Malikiyyah suke kai. Sannan mai binsa sai Hanafiyya saboda Qarfin hujjah da dalili.

Abinda yake Qara Qarfafar ra'ayin da Malikiyyah take kai shine hadisin da Abu Huraira ya ruwaito cewa Wani Mutum ya karya azuminsa acikin Ramadhan sai Manzon Allah (saww) ya umurceshi yaje ya 'yantar da kuyanga, ko yayi azumin wata biyu ajere, ko kuma ya ciyar da Miskinai sittin.

(Imamu Muslim da Malik ne suka ruwaito)..

Kunga kenan wannan hadisin ya nuna cewa babu bambanci tsakanin Jima'i ko cin abinci acikin Ramadhan (wajen wajibcin yin kaffarq idan akayi su da gangan). Domin kuwa duk wanda mutum ya aikata, to ya keta alfarmar Watan Ramadhana ne.

Allah ne Masani.

Alhamdulillah nan zamu tsaya sai akaratu na gaba.

AN GUDANAR DA KARATUN NE A ZAUREN FIQHU WHATSAPP (2014).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI