WACECE NANA FATIMAH?

AN HAIFI SAYYIDAH FATIMAH (A.S) acikin garin Makkah, ranar 20 ga watan Jumaada akhir, ashekara ta biyar bayan Manzanci. Wato shekara 8 kafin hijra. (kamar yadda yazo acikin "SIYARU A'ALAMIN-NUBALA'I.

Ta taso cikin kyakkyawar tarbiyyah wacce babu kamarta. Kasancewar Mahaifiyarta ita ce Nana Khadeejah bintu Khuwailid (rta) wacce ta zamto Mafificiya acikin Matayen Zamanin da, harma na yanzu.

Mahaifinta kuwa shine Shugaban dukkan Annabawa da Manzanni (saww). Kuma shine mafificin halittu ta wajen kyawun hali da dabi'u.

Nana Fatimah fara ce kyakkyawa mai kyawun diri. Tafi kowa daukar kamannin mahaifinta. Tayi kama dashi wajen zamansa da tashinsa da tafiyarsa da maganarsa da murmushinsa.

Nana Fatimah ta taso da kaifin hankali da basira wacce ta zarce sauran tsararrakinta. Don babu tamkarta acikin Matayen zamaninta.

Ta kasance tana taimakon mahaifinta wajen isar da sakon Allah, Kuma duk da kasancewarta yarinya Qarama alokacin, takan nuna fushinta akan abinda kafirai suke yiwa mahaifinta.

Tana da kyawu da kwarjini irin na Mahaifinta. Ga kuma yawan ibadah, ga tsoron Allah. Wannan yasa ta haye saman dukkan matayen Halittu awajen daraja da Mukami.

An daura aurenta mai albarka acikin shekara ta 2 bayan hijira. Wato bayan yakin badar. Kuma Allah ne ya aiko Mala'ikah Jibreelu da sakon cewar "Yana umartar Manzonsa (saww) da cewar ya aurar da ita ga Sayyiduna Aliy bn Abi Talib (rta)".

Amma a ruwayar da tafi shahara, ance Sayyiduna Aliyu ne da kansa ya nemi aurenta awajen mahaifinta, kuma ya amince ya bashi ita, bayan wasu daga cikin manyan Sahabbansa sun nema bai basu ba.

Ta haifi 'ya'ya biyar ne arayuwarta :

- Alhasan.
- Alhusain.
- Al Muhsin.
- Zainab.
- Ummu Kulthum.

kuma ta rasu ne agarin Madinah Acikin shekara ta 11 bayan hijira, wato wata 6 bayan wafatin mahaifinta (saww).

Kuma an binne ta ne a Makabartar BAQEE'A, inda aka binne sauran 'Yan uwanta wadanda suke rigata rasuwa.

TA RAYU SHEKARU 28, ko kuma 27  aduniya. (kamar yadda Imam At-Tabraaniy ya ruwaito acikin "ALKABEER" juzu'i na 22 shafi na 399 hadeeth mai lamba 997.

'Ya'yanta wadanda suka rayu abayanta, Akwai Alhasan bn Aliy bn Abi Talib (rta) ya rayu lokaci mai tsawo har sai da ya zama Khalifa na biyar daga cikin Halifofi shiryayyu.

Ya hau kujerar Khalifanci bayan Mahaifinsa, kuma watanni shida yayi sannan ya sauka ya bar ma Sayyiduna Mu'awiyah (ra).

Shi kuwa Sayyiduna Al-Husain ya rayu har zuwa shekara ta Sittin da daya (61) bayan Hijira. Yayi shahada ne akusa da garin Karbala, aranar 10 ga Almuharram.

Ita kuma Ummu Kulthum lokacin da ta isa aure, Mahaifinta (Imam Aliyu) ya aurar da ita ga Sarkin Muminai Umar bn Al-Khattab (rta).

Lokacin da Sayyiduna Umar (ra) ya aureta, ya shigo Masallacin Manzon Allah (saww) yana murna, ya tarar da Sahabbai Muhajiruna suna zazzaune, yace musu "Kuyi mun murna. Domin hakika ni na auri Ummu Kulsum 'yar Aliyu bn Abi Talib. Kuma hakika ni naji Manzon Allah (saww) yana cewa :

"KOWACCE NASABA DA DALILI DA SURKUNTA YANA YANKEWA ARANAR ALQIYAMAH SAI DAI ABINDA YA ZAMA DAGA NASABATA DA DALILINA DA SURKUNTANA".

Ita kuma Zainab (rta) Sayyiduna Aliyu ya aurar da ita ne ga 'Dan yayansa mai suna Abdullahi bn Ja'afar bn Abi Talib (rta).

Allah shi Qara girma da aminci da daukaka ga Nana Fatima 'Yar Ma'aikin Allah. Matar da ta fifici dukkan matayen Halittu baki daya.

Wannan rubutun sakon gaisuwa ne daga Zauren Fiqhu zuwa ga dukkan Shurafa'u 'ya'yan Nana Fatimah, da dukkan masoyanta baki daya.

BUKATATA : Kuyi min shaida agaban Allah cewa ni Masoyinta ne.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI