HADISINMU NA YAU (03 GA RAMADHAN 1437)

Hadisin namu na yau yana kunshe da wata Qissah ce mai ratsa jiki. An karboshi daga Sayyiduna Abu Sa'eed Al-Khudriy (Malik bn Sinaan) Allah shi yarda dashi. Shi kuma ya karbo daga Manzon Allah (saww) yace:

"Ya kasance acikin al'ummar da suka gabaceku akwai wani mutum wanda ya kashe Rayuka guda Chasa'in da tara (99). Sai yayi tambaya cewa (Yana so a nuna masa) Mutumin da yafi kowa Ilimi adoron Qasa, sai aka nuna masa wani Mutum mai bautar Allah.

Sai ya Qarasa wajensa yace masa Shi ya kashe rayuka guda 99. Shin (Allah) zai karbi tubansa kuwa?". Sai wannan mai bautar Allah din yace masa "A'a". Don haka sai ya kasheshi ya cika 'dari (100) dashi.

Sannan sai ya sake tambaya akan anuna masa Wanda yafi kowa Ilimi adoron Qasa. Sai aka nuna masa wani Mutum Malami. Sai ya gaya masa cewa Shi ya kashe rayuka guda 'dari (100). Shin za'a karbi tubansa kuwa?.

Sai Malamin yace masa "Kwarai kuwa. Waye ya isa shiga tsakaninsa da tsakanin Tuba?. Ka tafi zuwa gari Kaza-da-Kaza. Domin acikinta akwai wasu Mutane masu Bautar Allah. Kaje ka bauta ma Allah tare dasu. Amma kada ka komo Qasar nan taka. Domin ita Mummunar Qasa ce".

Sai ya tafi har sai da yakai kusa rabin hanyar sai mutuwa tazo masa. Sai Mala'ikun Rahama da Mala'ikun Azaba sukayi jayayya akansa (Wato suna jayayya akan shin waye daga cikinsu zai dauki ransa).

Mala'ikun Rahama suka ce "Ya taho ne domin tuba. Kuma ya fuskanci Allah da zuciyarsa". Su kuma Mala'ikun Azabar sai suka ce "Ai shi bai ta'ba aikata alkhairi ba, tunda yake".

Sai wani Mala'ika yazo musu acikin siffar 'Dan Adam, Sai suka sanyashi atsakaninsu, Wato amatsayin mai yin hukunci. Sai yace musu "Ku auna tsakanin Qasashen nan guda biyu. Duk wacce yafi kusa da ita, to ita ce tasa".

Da suka auna sai suka tarar cewa yafi kusa da Qasar da yayi niyyar tafiya din nan. Don haka sai Mala'ikun Rahama suka karbeshi (wato suka karbi ransa kenan).

Acikin wata ruwayar Imamul Bukhariy kuma, cewa akayi  "Sai ya kasance yafi kusa da Garin mutanen kirkin nan da gwargwadon tsawon tafin hannu, Don haka sai aka sanyashi acikin mutanenta".

Acikin wata ruwayar kuma acikin Sahihul Bukhariy, an ce "Sai Allah Madaukakin Sarki yayi wahayi zuwa ga wannan Qasar cewa "KI NESANTA DASHI". Sannan yayi wahayi zuwa ga waccen Qasar ita kuma "KI KUSANTO GARESHI".

Sannan yace "KU AUNA TSAKANINSU". Sai aka tarar yafi kusa da wannan din da gwargwadon tsawon tafin hannu, don haka aka gafarta masa".

Acikin wata ruwayar kuma "Sai ya juyar da Qirjinsa zuwa wajenta".

HADISI NE SAHIHI, ADUBA :

- Sahihul Bukhariy hadisi na 3470.
- Sahihu Muslim hadisi na 2766.

BAYANI
********
Wannan hadisin yana karantar damu abubuwa da dama. Daga cikinsu akwai :

1. FIFIKON ILIMI AKAN IBADAH : Da kuma Fifikon Malami akan Jahili mai yawan ibadah. Domin kuwa wancan na farko din Jahili ne mai yawan ibadah, bai san Allah ba, kuma bai san yawan falalar Allah ba. Shi aganinsa kamar Allah ba zai yafe ma mutumin nan ba. Kunga yayi ma Allah karambani kenan. Da yawa daga cikin mutanen zamanin nan sukan yi ma Allah irin wannan karambanin ta hanyar kafirta Musulmai ko kuma cewa su wane 'Yan wuta ne. Alhali basu da hakikar sani akan hakan.

2. MUHIMMANCIN TUBA : Komai yawan zunubinka bai kamata ka fidda tsammanin samun rahamar Allah ba. Shi Allah mai rahama ne, mai jin kai ne. Kuma masoyin bayinsa ne. Yana karbar tubansu aduk sanda suka nemi yafewarsa.

Kamar yadda Allah ya gafarta ma mutumin nan wanda ya kashe rayuka guda 100, kaima Allah yana iya gafarta maka komai yawan laifinka. Kai dai kar kayi jinkiri, Kar ka sakankance, Kada kuma kayi tuban Muzuru.

3. WAJIBCIN KAURACE MA MUTANEN BANZA : Lallai wannan hadisin ya nuna cewa mutukar kana so Allah ya amshi tubanka, to lallai sai ka guji zama da mutanen banza.

4. MUHIMMANCIN KUSANTAR MUTANEN KIRKI : Tunda gashi an gafarta masa saboda kusancinsa da garin mutanen kirki. lallai ya kamata kowanne Mutum Mumini ya zama yana tare da abokai na kirki, sannan ya nemi jagoran addini na kirki (Wato Malami mai shiryarwa). Domin kusanci da mutanen kirki yakan sanya mutum ya samu alkhairan da bai ta'ba tsammani ba.

5. HIKIMA IRIN TA ALKALANCI : Wannan ya nuna mana cewar duk lokacin da Alkali yaga abubuwa sun rikice masa, zai iya bullowa da wata hanya ta hikima domin warware rigimar da ake ciki.

6. GIRMAN AFUWAR ALLAH DA KUMA SOYAYYARSA GA BAYINSA : Ku dubi yadda Ubangiji yayi wahayi zuwa ga garin Mutanen banza din cewa ya nisanta, Kuma yayi wahayi zuwa ga garin mutanen kirkin cewa ya kusanto. Lallai wannan ya nuna mana cewar lallai Komai girman laifinka, to afuwar Allah da Soyayyarsa ta fishi girma.

Ina fatan dukkan daliban Zauren Fiqhu zasu rika katanta wadannan jerin hadisai cikin nutsuwa, kuma suna karantar dashi ga abokansu da iyalansu domin mu gudu tare, mu tsira tare.

Allah yasa mu dace. Ameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (03-09-1437) 08-06-2016.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI