MATA FITINAR DUNIYA

MATA FITINAR DUNIYA
*************************
"YANA DAGA CIKIN AYOYINSA, YA HALICCI MATA DAGA GAREKU, DOMIN KU SAMU NUTSUWA ZUWA GARESU, KUMA YA SANYA SOYAYYA DA TAUSAYI ATSAKANINKU. HAKIKA ACIKIN WANNAN AKWAI ABIN LURA GA MUTANE MASU TUNANI".

Acikin wannan ayar Allah ya bayyana mana ainihin dalilin da yasa ya halicci mata daga garemu kuma ya sanya suka zama abokan zamanmu.

Acikin wata ayar kuma yace: "YA KU MUTANE KUJI TSORON UBANGIJINKU WANDA YA HALICCEKU DAGA RAI KWAYA 'DAYA, KUMA YA HALICCI ABOKIYAR ZAMANTA DAGA GARETA, KUMA YA FITAR DA MAZAJE MASU YAWA GARESU DA KUMA MATAYE".
(Suratun Nisa'i ayah ta 1).

Ibnu Katheer ya rubuto acikin littafin Tafseer dinsa cewa "Yayin da Annabi Aadam (as) yake barci agidan aljannah akan ciri Qashin Hakarkarinsa na dama, aka halicci Nana Hauwa'u dashi.

Yayin da ya farka daga barcinsa, ya ganta kuma ya samu nutsuwa daga gareta, itama ta samu nutsuwa daga gareshi.

Amma lokacin da Iblees (L. A) yazo domin yaudararsu, ya biyo ta wajen Nana Hauwa'u ne. Kamar yadda Ibnu Jareer At-Tabariy ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi 'dan Abbas (ra) yace "Bayan Annabi Aadam (as) yaci daga bishiyar nan wacce Allah ya haneshi, sai Allah ya tambayeshi "YA AADAMU MAI YASA KACI DAGA WANNAN BISHIYAR WACCE NA HANEKA?".

Sai yace "(Ya Ubangiji) Ai Hauwa'u ce ta umurceni".

Sai Ubangiji yace masa "To lallai ni zanyi mata Uqubah cewa ba zata dauki ciki, sai acikin Wahala. Kuma ba zata haihu ba, sai cikin wahala".

Acikin littafin Imamul Qurtubiy kuma, ce mata akayi "Kamar yadda kika jima bishiyar nan rauni, to hakanan Jini zai rika fito miki kowanne Wata. Hakanan kuma zaki rika daukar ciki kina haihuwa acikin wahala".

Lokacin da Allah ya sauko dasu duniya, Shi Annabi Aadam (as) ya sauka acikin yankin Qasar India ne. Har ma ya taho da wasu ganye daga bishiyoyin Aljannah. Ta wannan dalilin ne aka samu bishiyoyin Turare suka tsiro sosai ayankin. Wasu sun ce shine yankin Kashmir na yanzu.

Ita kuma Nana Hauwa'u ta sauko ne ayankin garin Jeddah ta Qasar Saudi Arabia. Anan ta zauna na tsawon shekaru har zuwa lokacin da suka hadu da Annabi Aadam (as) akan dutse 'Arfah.

Shi kuma Iblees acikin wata ruwayar ya sauka ne awajejen Dagistan, ayankin Russia. Ita kuma Macijiyar nan wacce yayi amfani da ita don samun nasara akan Nana Hauwa'u, ana jefota ne ayankin Asbahaan.

Nana Hauwa'u taci gaba da haihuwar Tagwaye ne Mace da Namiji. Kuma zunubin farko wanda aka fara yiwa Allah adoron Qasa, shine hassadar da 'dan Annabi Aadam (as) mai suna Qabila yayi ma 'dan uwansa mai suna Haabila. Kuma sanadiyyar abun akan Mace ne.

Haka abin yayi ta tafiya har zamanin sauran Annabawa, Mata sukan zama sanadiyyar tashin rigingimu da yakoki wanda akan rasa dubunnan rayuka.

Ku dubi Annabi Nuhu (as) shekaru dari tara da hamsin (950) yayi yana Wa'azi acikin al'ummarsa, amma Matarsa ba tayi imani dashi ba. Hasali ma ita take gaya ma mutane cewa "Wai shi Mahaukaci ne". Awata ruwayar kuma idan taga mutum yayi imani dashi sai taje ta sanar ma manyan kafiran garin, su kuma sai su tilasta masa ya koma kafirci.

Ku dubi matar Annabi Luut (as) itama yadda ta ha'inceshi acikin addini. Ta kasance idan taga ya sauki baqi agidansa sai ta sanar ma Kafiran garin, masu aikata Luwadi suzo su kamasu da Qarfi.

Kunga dai kirki irin na Annabawa (as) da kyawun hali irin nasu amma basu tsira daga sharrin Mata ba. Don haka duk kudinka ko sarautarka ko malumtakarka, ba zaka tsere daga sharrinsu ba.

Annabi Yahya (as) wata karuwa ce daga Karuwan Banu Isra'eel tasa aka kasheshi, aka bata kansa. (Allah ya la'anceta).

Haka al'amarin yake har yanzu. Shi yasa Manzon Allah (saww) yace : "BAN BAR MA MAZA WATA FITINA WACCE TAFI CHUTAR DASU BA, FIYE DA MATA".

Wato mata sune fitina mafi girma wacce tafi chutar da Mazaje. Rayuwa ba zatayi da'di sosai ba, dole sai dasu.  Sannan kuma idan ana tare dasu ba za'a gushe cikin damuwa, bacin rai, hayaniya,  Makirci, da sauran sharruka irin nasu ba.

Matan aure kuwa Manzon Allah (saww) cewa yayi "HAKIKA ITA MACE AN HAKICCETA NE DAGA QASHIN HAKARKARI. KUMA MAFI KARKACEWAR ABU AJIKIN HAKARKARI SHINE SAMANSA.

IDAN ZAKA JI DA'DI DA ITA, TO KAJI DA'DI DA ITA ALHALI TANA TARE DA WANNAN KARKACEWAR.

IDAN KA NEMI SAI KA MIKAR DA ITA, TO ZAKA KARYA TA". (SAKINTA SHINE KARYEWARTA).

(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).

Acikin wani hadisin kuma ya nuna mana cewa Su Mata raunana ne, Amma sukan rinjayi babban mutum. Su kuma Qankanin mutum yakan rinjayesu.

Sune manya daga cikin rundunar Iblees. Yakan yi amfani dasu wajen dulmiyar da wasu da yawa daga cikin Banu Aadam.

Saboda rauninsu shi yasa Manzon Allah (saww) yayi ma mazaje wasiyyar cewa lallai su rikesu cikin kyautatawa da mutuntawa. Kuma ya bama Mazaje ragamar daukar nauyinsu.

Amma Mace idan ta tsaya bisa hanyar Allah takan zama dalilin shiryuwar al'ummah masu yawa. Musamman idan anyi la'akari da yanayin sanyin hali irin nasu da kuma kaifin basirar fahimtar halayen yara, ko Mazajensu da suke dashi.

Manzon Allah (saww) ya Qirga mace tagari acikin manyan kayan jin dadin rayuwar duniya. Sannan koda agidan Aljannah, mata suna daga cikin abubuwan jin dadin da Allah ya tanadar ma bayinsa Muminai.

Allah shi bamu Mata nagari, ya gyara halayen wadanda muke tare dasu, ya inganta tarbiyyar yaranmu. Allah yasa su zama ni'ima agaremu ba fitina akanmu ba.

DAGA ZAUREN FIQHU (07064213990) 14-09-1437 (19-06-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI