MAGANIN CIWON TSAKUWAR UWAR HANJI

TAMBAYA TA 2021
********************
Assalamu alaikum Zauren Fiqhu, fatan alkhairi da godiya ga Malam. Ni dalibi ne a wannan zaure mai albarka na shafin facebook, Ina fama da wani irin ciwon ciki ne wanda idan ya rike ni ko tashi tsaye inyi tafiya mai kyau bana iyawa, kuma nayi scanning har sau uku amma ba komai take nunawa ba, sai yau danayi awani asibitin sukayi confirming appendixes ne. Don  Allah Malam ban Sani ba ko akwai wasu magungunan da zan iya amfani dasu Wanda ba sai anyimin operation ba. JAZAKUMALLAH BI AHSANUL KHAIR.

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Da farko dai muna yi maka fatan alkhairi da fatan Allah ya baka lafiya daga dukkan abinda ke damunka.

Akwai abubuwa da dama a likitancin Musulunci wadanda sukan magance irin wannan ciwon in sha Allahu. Kamar yadda bayanai suka gabata anan Zauren Fiqhu. Ga wasu nan kamar haka :

1. Ka samu Garin Kustul Hindi cokali 7, garin Shammar cokali 7, Garin Habbatus sauda cokali 7, garin Kirfa cokali uku. Ka gaurayasu baki daya acikin zuma mai kyau (Farar saqa).

Zaka rika shan cokali uku safe da rana da yamma har tsawon kwanaki 30.

2. Man Tafarnuwa, Man Habbatus sauda, Man Jirjir, Ka hadasu waje guda. Sannan ka samu shayin Na'a-Na'a mai kyau, Ka rika zuba wancan hadadden man cokali 2 acikinsa kullum da safe ka rika shansa da zuma.

Zaka sha har sati biyar (5 weeks).  in sha Allahu zaka samu waraka daga Matsalar da ta shafi hanji kamar:

- Typhoid Fever (Zazzabin hanji).
- Ulcers (wato Olsa, gyambon ciki).
- Indigestion (wato Magwas).
- Appendicitis (Tsakuwar ciki).
- Majinar Qirji, da Majinar ciki.
- Piles (Basur mai sa kumburin ciki, ko kaikayin dubura).

3. ZAM-ZAM : Ka rubuta ayatush Shifa'i da tawada mai tsarki, ko kuma ka tofa Qafa bakwai tare da Fatiha 1 da Qul Huwallahu kafa 11 acikin ruwan zam-zam ka rika sha kullum har sati uku.

In sha Allahu zaka samu waraka daga abinda ke damunka ko menene, albarkacin Alqur'ani.

Allah ya sawwake, Allah shi baka lafiya tare da dukkan Musulmai masu jinya.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 08163621213 (08-02-1438) 08-11-2016.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI