YA SAKETA ACIKIN IDDAH

YA QARA SAKINTA ACIKIN IDDAH

TAMBAYA TA 2025
*******************
Aslkm Wa rahmatullahi Wa barakatuhu. Don Allah zauren Fiqhu, Ina son a kara warware min wannan matsalan. Mijina ne ya ce nasakeki saki daya, toh ina cikin wancan iddah ban kare ba sai yace ya kara daya. Shine nake son inji sakin na biyun yayi ko baiyi ba?.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Eh lallai ya halatta ga Mijinki ya Qara yin wani sakin bayan wannan na farkon da yayi, koda kina cikin iddah. Kuma sakin ya yiwu.

Da ache kin riga kin Qare iddar farko ne, to kin fita daga hannunsa baki daya. Bashi da wannan damar. Amma ayanzu kam wannan sakin ya yiwu.

Idan kika kammala jininki uku shikenan kina da damar kije ki auri wani sabon Mijin.

Allah ya sawwake, Allah ya daidaita tsakanin dukkan Ma'auratan da suke cikin rikici.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 14-11-2016 (14-02-1438).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI