HALAYEN MASU TSORON ALLAH (02).
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Ya Allah yi salati da aminci mafi wanzuwa bisa Babban Masoyin nan naka wanda babu kamarsa. Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa amintattu, da Sahabbansa masu daraja. Daliban Zauren Fiqhu, wannan shine darasi na biyu acikin Maudhu'in da muke bayani akan Halaye ko kuma dabi'un magabata na kwarai dangane da yadda tsoron azabar Allah ako yaushe. Duk da cewar su din mutane ne masu mutukar Son Allah da Manzonsa da kuma tsayawa akan ibadah dare da rana. Kuma muna fadin halayensu ne domin muji muyi amfani dashi, mu kwaikwayesu gwargwadon ikonmu. Yazeed bn Hushib (rah) yace: "Ban taba ganin mutane masu tsananin tsoron Allah kamar Hasanul Basariy da kuma Umar bn Abdil-Azeez ba. Saboda tsananin tsoron azabar Allah, kai kace dominsu kadai aka halicci Wutar!". Shi dai Umar bn Abdil-Azeez yana daga cikin Banu Umayyah. Kuma tun daga ranar da ya karbi Khalifancin daular Musulunci bai taba kwanciya yayi barcin dare akan katifarsa ba. Ya