DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) 2

DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) 2
*************************************
Babban Malamin Hadisin nan a Mazhabin Malikiyyah, wato Alqadhiy 'Iyadh ya ruwaito acikin ASH-SHIFA cewa :

Manzon Allah (saww) ya hau kan dutsen Thabeer Lokacin da Kafirai suke nemansa zasu kasheshi. Sai dutsen yayi magana dashi yace masa "Sauka Ya Rasulallahi. Domin ni ina tsoron kada su kasheka akan bayana, Kuma Allah yayi mun azaba".

Shi kuma Dutsen Hira'u yace "Taho gareni Ya Ma'aikin Allah".

Dutsen Thabeer da Dutsen Hira'u makobtan juna ne. Suna daura da juna, amma akwai wani kwari atsakaninsu.

ADUBA ANWARUL MUHAMMADIYYAH ta Shaikh Yusufun Nabhaniy (rah) akan shafi na 275.

Kunji fa yadda duwatsu suke gasar nuna kishinsu da soyayyarsu gareshi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Kaima kayi hankali da zuciyarka kada ta rudeka ka rika jin Qaikayi azuciyarka idan kaji ambatonsa.. Domin hakika Imani ba ya tabbata sai da Tsantsar Soyayyar Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Salati da amincin Allah su tabbata agareshi da iyalan gidansa da Sahabbansa bisa gwargwadon Matsayinsa da Muqaminsa awajen Ubangijinsa (SWT).

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (05-11-2017 16-02-1439).

www.zaurenfiqhu.com

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI