HALAYEN MASU TSORON ALLAH (02).

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Ya Allah yi salati da aminci mafi wanzuwa bisa Babban Masoyin nan naka wanda babu kamarsa. Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa amintattu, da Sahabbansa masu daraja.

Daliban Zauren Fiqhu, wannan shine darasi na biyu acikin Maudhu'in da muke bayani akan Halaye ko kuma dabi'un magabata na kwarai dangane da yadda tsoron azabar Allah ako yaushe. Duk da cewar su din mutane ne masu mutukar Son Allah da Manzonsa da kuma tsayawa akan ibadah dare da rana.

Kuma muna fadin halayensu ne domin muji muyi amfani dashi, mu kwaikwayesu gwargwadon ikonmu.

Yazeed bn Hushib (rah) yace: "Ban taba ganin mutane masu tsananin tsoron Allah kamar Hasanul Basariy da kuma Umar bn Abdil-Azeez ba. Saboda tsananin tsoron azabar Allah, kai kace dominsu kadai aka halicci Wutar!".

Shi dai Umar bn Abdil-Azeez yana daga cikin Banu Umayyah. Kuma tun daga ranar da ya karbi Khalifancin daular Musulunci bai taba kwanciya yayi barcin dare akan katifarsa ba.

Ya tara matayensa da kuyanginsa yace musu to shifa yanzu babban aiki ya sameshi. Don haka yanzu bashi da wani lokaci dominsu. Wace taga zata iya zama dashi ahaka, to shikenan.

Matarsa ma 'Yar Baffansa ce. Wato mahaifinta ya taba zama khalifan daular Musulunci. Kuma har ya bata sarkoki da kayan ado na alfarma. Amma Umar bn Abdil-Azeez duk ya karbe ya mayar dasu acikin Baitul-Malin al'ummah.

Kullum kwana yakeyi yana Sallah yana kuka, har sai gemunsa ya jike sharaf da hawaye, har sai ya jike wajen da yake tsaye yana sallar.

Awasu Sannan kuma yakan zagaya cikin gari yana lekawa cikin kowannd lungu domin kiyaye lafiyar al'ummar da yake mulki.

Saboda tsantsar adalcinsa acikin shekaru biyun da yayi yana Mulki, sai da ya zamto 'barayi sun dena sata. Kura ta dena kama awakai da tumakin mutane. Kai hatta Macizai acikin daji sun dena cizon Mutane.

Sai da ya zamanto idan ka fito da zakkar Zinare ko Azurfa ko kayan abinci zai yi wahala ka samu wanda zai karba. Saboda kowa ya riga ya zama mawadaci.

In sha Allahu nan gaba anan Zauren Fiqhu Facebook da Whatsapp zamu ware wani lokaci na musamman domin yin nazari acikin tarihin wannan babban Gwarzo Umar bn Abdil-Azeez (rta).

Al-Harith bn Hisham yace "Watarana naje in gaisar da Abdullahi bn Hanzalah bashi da lafiya, sai wani mutum ya karanto wata ayah agabansa wacce take cewa :

لهم من جهنم مهاد ومن فوقهم غواش.

"('YAN WUTA) SUNA DA WATA SHIMFIDA DAGA JAHANNAMA, KUMA DAGA SAMANSU AKWAI WANI MURFI".

Nan take sai abdullahi bn Hanzalah ya rika zabga kuka har sai da nayi tsammanin ko ransa ne zai fita.. Yana kuka yana cewa :

"SHIKENAN SUN ZAMANTO ACIKIN FAYA-FAYEN WUTAR JAHANNAMA!".

Yana ta kuka, sai muka ga ya tashi ya tsaya da kafafunsa. Sai wani mutum yace masa "Ya kai Abu-Abdillah!! Ka zauna (tunda baka da lafiya)".

Sai yace "Ai ba zan iya zama ayanzu ba. Wannan tunanin Wutar ba zai barni in iya zama ba, Ban sani ba, ko nima ina daga cikinsu!!".

Abdurrahman bn Mus'ab (rah) yace "Wani mutum (daga cikin Magabata na kwarai) ya kasance yana tsaye akan gefen Kogin Furaat (sunan wani kogi ne akasar Iraq) sai yaji wani mai karatu yana cewa:

إن المجرمين في عذاب جهنم خالدون "

"HAKIKA MASU LAIFI ZASU DAWWAMA NE ACIKIN AZABAR JAHANNAMA".

Daga jin haka sai wannan mutumin (na gefen kogin) yayi wata irin Hajeejiya yana layee.

Lokacin da wancan Mutumin  (mai karatun) ya karanto ayar dake gaba da wannan din :

"لا يفتر عنهم و هم فيه مبلسون"

"BA ZA'A SASSAUTA MUSU BA, KUMA HALIN KASANCEWARSU MASU FIDDA TSAMMANI ACIKINTA (WATO SUN GAMA FITAR DA TSAMMANIN SAMUN WANI SAUKI KO RANGWAME ACIKIN AZABAR).

Yana karanta wannan ayar sai aka ga wancan din hajijiyar nan ta jefashi acikin Kogin.. Anan ya nutse ya mutu. (Allah ya rahamsheshi).

'Yan uwa kunji fa halayen masu tsoron Allah. Idan sunji ayar azabah sai su Gigice har su fita daga hayyacinsu.

Fudhayl bn Iyaadh (rah) yana daga cikin magabata na kwarai. Kuma yana da tsananin tsoron Allah. Hakanan yana da wani Yaro 'dansa na cikinsa mai auna Aliyu. Shima haka yake kamar Mahaifin nasa.

Abubakrin bn 'Ayyaash (rah) yace : "Nayi sallar Maghriba abayan Fudhayl bn Iyaadh (rah) amma agefena acikin Sahu akwai 'dansa mai suna Aliyu.

Bayan karatun Fatiha sai ya dauko surar ALHAKUMUT TAKATHUR". Amma yayin da ya iso kar ayar nan wacce Allah yake cewa :

لترون الجحيم

"WALLAHI SAI KUN GA WUTAR NAN TA JAHEEM".

Yana karanta wannan ayar sai naga Aliyu din ya fadi Qasa ya suma!! Shi kuma Fudhaylu ya kasa wuce kan ayar. Yana ta maimaitawa yana kuka... Da haka har ya idar da sallar. Yayi mana sallah irin ta masu tsananin tsoron Allah.

Naci gaba da zama awajen shi Aliyun (wanda ya suma) amma bai farfado ba, sai chan tsakiyar dare!!!".

'Yan uwa kunji fa! Ayah guda daya RAK aka karanta agabansa amma ya fadi Qasa ya suma tun da Maghriba Bai farka ba sai tsakar dare.

Wadannan fa sune hakikanin bayin Allah nagari. Masu kwadayin rahamarsa da kuma tsoron azabarsa.

Ba irin mutanenmu na yanzu ba. Wanda zaka ji Malami yana karatu, yana ta jan ayoyi amma ba ya aiki dasu. Yana karanta hadisai amma ba ya tsayawa yin tunani akan Ma'anoninsu ballantana yayi aiki dasu.

Kaji Malami kullum shi ba zai iya yin Wa'azi bai zagi wasu jama'a ba.. Wai shi dole sai kowa ya dawo kan fahimtarsa!!!

Wallahi Jama'a sai mun bi ahankali.. Ba'a koyi da Malami saboda zaqin bakinsa, ko kuma saboda Qungiyanci ko bangaranci.. A'a ana koyi da Malami ne saboda tsoron Allahnsa, gudun duniyarsa, Yawan ibadarsa, Rikon amanarsa, Gaskiyar zancensa, etc.

Ya kamata wallahi mutane mu FARKA, mu tashi mu nemi ilimin addini. Mu dena kyale wasu jama'a su mayar damu tamkar kwallon kafa. Yau an jefaka nan. Gobe kuma an jefaka chan!! Gara mu tashi mu koma zaure, mu nemi ilimi awajen masu shi.

Bayin Allah na kwarai basu da lokacin zagi ko cin mutuncin wani.. Domin tunanin laifukansu na kansu ma ya ishesu aiki. Ballantana su tsaya hangen laifin wasu.

Wannan nasiha ce ga dalibanmu na zauren fiqhu tare damu baki daya. Allah yasa mu dace. Aaameeen.

An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP -3 da misalin Qarfe 12:00pm (24-11-2015).

Comments

  1. Amin ya hayyu ya qayyum Dan Allah a taimaka a sakani a group na WhatsApp 08163357478 Allah ya saka da alkhairi

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI