RANAR DA YABAR DUNIYA (2)

RANAR DA YA BAR DUNIYA (2)
*******************************
Sayyiduna Anas bn Malik (ra) ya ruwaito cewa "Yayin da Annabi (saww) jinyarsa tayi nauyi, ya kasance Zafin ciwo yakan lullubeshi.

Sai Nana Fatimah (as) tace "WAYYO WAHALAR BABANA!!".

Sai Annabi (saww) yace mata "BAYAN YAU DIN NAN BABU SAURAN WATA WAHALA AKAN BABANKI".

Yayin da Annabi (saww) ya rasu, sai Nana Fatimah tace "Wayyo Mahaifina! Ya amsa kiran Ubangijin da ya kirashi!... Wayyo Mahaifina! Aljannar Firdausi ce Masaukinsa. Wayyo Mahaifina, Zuwa ga Mala'ika Jibreelu muke mika Ta'aziyyarsa!".

Yayin da aka binneshi kuma sai Nana Fatimah tace ma Sahabbai "Shin Zukatanku sunyi muku da'di yayin da kuka Watsa Qasa bisa Manzon Allah (saww) ?".

Imamul Bukhariy ne ya ruwaitoshi.

Allahu Akbar!!! Nana Fatimah muna yi miki Ta'aziyyar Abbanki wanda babu Musibar da tafi rashinsa girma akan Mumini mai cikakken imani.

Tunda ake rasuwa ba'a ta'ba yin irin tasa ba.. Duniya bata ga tamkarsa ba, ballantana ta sake samun irinsa.

Amincin Allah ya tabbata agareka Ya Rasulallahi aranar da kazo duniya, da ranar komawarka zuwa ga Ubangijinka, da kuma ranar da Qasa zata tsage ka fito domin bayyanar Matsayinka..

DAGA ZAUREN FIQHU (21-08-1438 18-05-2017).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI