ƊAUƘAR CIKIN MANZON ALLAH (SAWW) DA KUMA HAIHUWARSA.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salati Matabbaci da aminci wanzajje su tabbata ga Mafi tsarkin dukkan bayi, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa. Acikin wancan darasin namu na farko, wanda muja gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp (3) munji Tarihin iyaye da kakannin Manzon Allah (saww) da yadda tsarkin nasabarsa take. Acikin wannan darasin kuma, in sha Allahu zamu ji abubuwan da suka faru tun daga daukar cikinsa har zuwa haihuwarsa (saww) da kuma abubuwan da mahaifiyarsa mai daraja ta gani na ayoyin Ubangiji da kuma girmamawa. Babban Malamin tarihin nan mai suna Ibnu Sa'ad (rah) ya ruwaito wani hadisi daga 'Yar uwar mahaifin Yazeed bn Abdillahi bn Wahab bn Zam'ah, tana cewa: "Lokacin da mahaifiyar Manzon Allah (saww) (Wato Aaminatu bintu Wahbin) ta dauki cikinsa, ta kasance tana cewa: "Ban san cewa ni ina dauke dashi ba. Kuma ban ji irin nauye-nauyen nan da Mata suke ji ba. Sai dai kawai ni ban ga al'adata ba. Kuma dama ta kas