IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA

Da Sunan Allah Buwayi gagara-misali, Mai kula da lamarin bayinsa. Wanda gyangyadi bai ta'ba daukarsa ba, ballantana barci. Babu abinda ke buya gareshi daga ayyukan bayinsa acikin sarari ko duhun dare.

Salati da aminci su tabbata ga Annabin da Allah ya aikoshi zuwa ga dukkan halittu amatsayin rahama garesu tare da gargadi da bushara, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mutanen kirki.

Wannan ita ce fitowa ta goma sha bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu wanda ke bayani dalla-dalla game da wasu al'amuran tashin alqiyamah wacce lamarinta ke kwankwasar zukata.

Babban abinda ya kamata mao karatu yayi, shine ya rika kwatanta faruwar abun a zuciyarsa domin hakika ranar nan tana tafe, kuma zata afku ne babu zato balle tsammani.

Hakika idan alqiyamah ta tsaya, awannan ranar akwai masifar zafi da Qunar rana saboda kusanto da ita da za'a yi. Mutane da Aljanu gaba dayansu zasu rika zubda gumi (wato zufa) wanda sai damshinsa ya kai zurfin zira'i saba'in a Qasa. Sannan ta sama kuma, kowa guminsa zai kamashi ne bisa gwargwadon yawan zunubinsa.

Akwai wanda guminsa zai kamashi zuwa idonsa sawayensa, akwai wansa nasa zai zo masa iya gwiwarsa, wani zuwa cibiyarsa ko kirjinsa, wasu kuma sai guminsu ya hadiyesu saboda miyagun ayyukan da suka aikata anan duniya.

Shi yasa wasu daga magabata na kwarai idan suka juyo daga sallar Juma'a acikin zafin rana, sukan fashe da kuka saboda wannan yana tuno musu da abinda zai faru aranar Alqiyamah bayan an gama yiwa mutum hisabi, zai juya acikin zafin rana zuwa ga masaukinsa na dindindin.. Kodai zuwa ga Aljannah madaukakiya cikin yardar Ubangiji, ko kuma zuwa ga Jaheemu da Hawayiwa cikin fushin Ubangiji tare da azaba mai wulakantarwa (Allah shi kiyayemu). Domin tabbas Alqiyamah zata afku ne aranar wata Juma'a wacce bata da asabar.

Wannan yinin ba zai rabe ba fache sai 'Yan Aljannah sun kasance cikin Aljannarsu, 'Yan wuta ma sun shiga masaukinsu. Wasunsu suna cikin ramin nan na Wailun, ko Gayyu, wasu kuma suna daure cikin sasari da Qukumi, wasu kuma an ratayesu suna shan bugu daga hannun Mala'iku tare da Quna marar yankewa. Babu hutu balle barci.. Ga tsananin yunwa da kishirwa kuma babu mai taimakonsa koda da digon ruwa balle abinci (Ya Allah ka kiyayemu don Qarfin ikonka).

Imamul Ghazaliy (Allah ya rahamsheshi) yace "Kuyi sani hakika duk wani gumin da baka zub dashi anan duniya ta dalilin shan wahalar neman ilimi ko Jihadi ko taimakon wani dan uwa musulmi ko wata hanyar neman yardar Allah ba, to hakika zaka fiddashi aranar Alqiyamah ta dalilin tsananin tsoro da jin kunyar Ubangijinka..". (Allahu Akbar!).

Wani daga cikin magabata yace "Da ache wannan ranar ta duniya zata fito koda sau daya ne bisa irin siffar yadda zata bayyana afilin Alqiyamah, Wallahi da sai dukkan duwatsun duniya sun narke, sai dazuzzuka sun Qone Qurmus, kuma sai Koguna da Tekuna duk sun Qafe".

Acikin wannan yanayin na zafi da matsi, Qishirwa zata tsananta ga Mutane da Aljanun dake tsaye awannan wajen. To amma kowanne Annabi yana da Tafki (Pond) wanda zai shayar da Muminan Al'ummarsa ka'dai. Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) shine wanda tafkinsa yafi na kowa girma. Tsawonsa ya kai kimanin tafiyar wata guda, haka ma fa'dinsa. Farinsa da haskensa wane Qankara!, Zakinsa ma ya zarce na zuma.

Al'ummarsa ne zasu rika gangarowa suna sha (Ya Allah ka sanyamu cikin mafiya samun babban rabo). Amma akwai wadanda koda sun gangaro sai Mala'iku koresu ba zasu sha ba. Saboda miyagun abinda suka aikata abayansa kamar riddah, bidi'o'i, chamfi, tsafi, kafirta musulmi, da sauran fitintunu acikin addini.

An tambayi Annabi (Alaihis salatu was salam) Ta yaya zaka gane al'ummarka awannan ranar?. Sai yace "Su suna da fararen gaɓɓai ne awannan ranar saboda guraben alwalarsu. Wanda ya kasance yana yawaita alwala da sujadah anan duniya, to awannan ranar shine haskensa zai fi yawa.

Ya Allah don albarkar falalarka da rahamarka ka gafarta zunubanmu ka shafe laifukanmu, ka rangwanta mana, Ka karbi tubanmu. Ka sanyamu cikin wadanda babu tsoro garesu awannan ranar kuma ba zasuyi bakin ciki ba.

Salati da aminci maras farko da karshe su tabbata bisa Annabinmu Shugabanmu Muhammadu mabudin rahama, tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa yardaddu. Da albarkar salatin nan Ya Allah ka sanyamu acikin mafiya samun kusanci dashi anan duniya da kuma ranar babban taro. Ameen.

AN GABATAR DA KARATUN NAN A ZAUREN FIQHU WHATSAPP RANAR 22/12/2018.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI