ƊAUƘAR CIKIN MANZON ALLAH (SAWW) DA KUMA HAIHUWARSA.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Salati Matabbaci da aminci wanzajje su tabbata ga Mafi tsarkin dukkan bayi, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa.

Acikin wancan darasin namu na farko, wanda muja gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp (3) munji Tarihin iyaye da kakannin Manzon Allah (saww) da yadda tsarkin nasabarsa take.

Acikin wannan darasin kuma, in sha Allahu zamu ji abubuwan da suka faru tun daga daukar cikinsa har zuwa haihuwarsa (saww) da kuma abubuwan da mahaifiyarsa mai daraja ta gani na ayoyin Ubangiji da kuma girmamawa.

Babban Malamin tarihin nan mai suna Ibnu Sa'ad (rah) ya ruwaito wani hadisi daga 'Yar uwar mahaifin Yazeed bn Abdillahi bn Wahab bn Zam'ah, tana cewa:

"Lokacin da mahaifiyar Manzon Allah (saww) (Wato Aaminatu bintu Wahbin) ta dauki cikinsa, ta kasance tana cewa:

"Ban san cewa ni ina dauke dashi ba. Kuma ban ji irin nauye-nauyen nan da Mata suke ji ba. Sai dai kawai ni ban ga al'adata ba. Kuma dama ta kasance takan dauke min kuma sai ta dawo.

Kuma wani mai zuwa yazo min atsakanin barci da farke, sai yace mun :

"SHIN KIN SAN KIN SAMU CIKI KUWA?"

Sai nace masa "A'a ban sani ba".

Sai yace min "HAKIKA KE KIN SAMU CIKIN SHUGABAN WANNAN AL'UMMAR KUMA ANNABINTA".

Kuma wannan abu ya faru ne aranar wata Litinin

Duk wannan yana daga abinda ya tabbatar min da cewa ina dauke da Juna.

Sannan sai ya jinkirta min har sai da Haihuwatata kusanto, sannan shi wannan mai zuwa din ya sake dawo min, sai yace:

"KICE INA NEMA MASA TSARI WAJEN ALLAH MAKADAICIN SARKI, DAGA SHARRIN DUK WANI MAI HASSADA"

Sai na kasance ina fadar hakan. (acikin wata ruwayar kuma, shi wannan mai zuwan ne yace masa "Kuma ki sanya masa suna MUHAMMADU".

Wannan Qissar tana nan acikin TABAQATUL KUBRA na Ibnu Sa'ad juzu'i na 1, shafi na 98.

Al-Imam Yusuf Bn Isma'il An-Nabhaniy ya kawi acikin Littafinsa mai suna AL-ANWARUL MUHAMADIYYAH MINAL MAWAHIBIL LADUNIYYAH acikin shafi na 20 zuwa na 21, shima yana cewa:

"Sahlu bn Abdillahil Tusturiy yace: "Yayin da Allah ya nufi sanya halittar Annabi Muhammadu (saww) acikin cikin Mahaifiyarsa, acikin watan Rajab ne. Sai ya umurci Mala'ika Ridhwanu (mai tsaron gidan Aljannah) cewa ya bude Kofofin Aljannah Firdausi. Kuma wani mai kira yayi kira acikin sammai da Qassai yana cewa:

"HAKIKA HASKEN NAN ABIN TASKANCEWA, BOYAYYE, WANDA DAGA SHI NE ANNABIN NAN MAI SHIRYARWA ZAI KASANCE, TO ACIKIN WANNAN DAREN NE ZAI TABBATA ACIKIN CIKIN MAHAIFIYARSA. WANDA ACIKINSA HALITTARSA ZATA CIKA. KUMA ZAI FITO ZUWA GA MUTANE YANA MAI BUSHARA KUMA MAI GARGADI".

Hakanan ya kawo wani hadisin daga Abdullahi bn Abbas (ra) yana cewa:

"Yana daga cikin alamomin samun cikin Manzon Allah (saww) cewa babu wata dabba daga dabbobin Quraishawa fache sai da ta bude baki tayi magana awannan daren. cewa : "Mun Rantse da Ubangijin Ka'abah, Lallai an dauki cikin Manzon Allah (saww) kuma shine Shugaban Duniya, kuma Fitilar Ma'abotanta".

Kuma babu wata kujera daga Kujerun Sarakunan duniya fache sai da ta wayi gari an Kifar da ita.

Imamu Ahmad da Imamul Baihaqiy sun ruwaito hadisi daga Al'irbaadh bn Saariyah (ra) Sahabin Manzon Allah (saww) yace Naji Manzon Allah (saww) yana cewa:

"NI BAWAN ALLAH NE, KUMA CIKAMAKIN ANNABAWA ALHALI (TUN ALOKACIN DA) ANNABI AADAMU YAKE CHUDANYE ACIKIN YUNBUNSA. KUMA ZAN BAKU LABARI AKAN HAKA:

"(NINE) ADDU'AR BABANA IBRAHEEM (AS) KUMA ANNABI EISA YAYI BUSHARA GAME DANI.

KUMA NINE MAFARKIN NAN DA MAHAIFIYATA TA GANI. KUMA HAKANAN DUKKAN MAHAIFAN ANNABAWA SUKAN GANI".

KUMA HAKIKA MAHAIFIYAR MANZON ALLAH (SAWW) YAYIN DA TA HAIFESHI TA GA WANI HASKE YA FITO DAGA GARETA HAR SAI DA YA HASKAKA KATANGUN BIRNIN SHAAM.

Aduba cikin : Musnadu Ahmad, juzu'i na 4 shafi na 127-128.

- MUSTADRAK na Hakim juzu'i na 2, shafi na 600. Kuma ya inganta isnadin hadisin.

- DALA'ILUN NUBUWWAH na Baihaqiy juzu'i na 1shafi na 80.

MAJMA'UZ ZAWA'ID na HAITHAMY juzu'i na 8 shafi na 223.

Imamu Ahmad da Baihaqiy da Tayyalisiy sun ruwaito daga Sayyiduna Abu Umamah Al-Bahiliy (ra) yace : "An tambayi Manzon Allah (saww) "Ya Rasulallahi shin menene farkon al'amarinka?".

Sai yace "ADDU'AR BABANA ANNABI IBRAHEEM (AS) DA KUMA BUSHARAR NAN TA ANNABI EISA (AS).

KUMA MAHAIFIYATA TAGA WANI HASKE YA FITO DAGA GARETA HAR SAI DA YA HASKAKA KATANGUN BIRNIN SHAAM".

Aduba :

- Musnadu Ahmad juzu'i na 5 shafi na 262

- DALA'ILUN NUBUWWAH juzu'i na 1 shafi na 84.

- MUSNADUT TAYYALISIY hadisi na 1140.

MAJMA'UZ ZAWA'ID na HAITHAMY juzu'i na 8 shafi na 222.

Mawallafin Littafin RAWA'IHUZ ZAKIYYAH acikin Shafi na 38 yace "Ruwaya ta tabbatar da cewa lokacin da aka haifi Manzonmu (saww) ya sauka ne adurkushe akan Gwiwoyinsa, sannan ya 'daga kansa yana kallon sama. Kuma wani haske ya fito tare dashi wanda sai da ya haskake katangun birnin SHAAM. Har sai da mahaifiyarsa ta rika hangen wuyan rakuman dake Busra".

(Ibnu Sa'ad juzu'i na1 shafi na 102).

Akan shafi na 39 kuma yace: "Abin nufi dai anan shine Hakika daren da aka haifi Manzon Allah (saww) dare ne mai girman daraja, mai yawan albarka, kuma mai bayyanannen Haske.

Dare ne wanda acikinsa ne Allah madaukakin sarki ya fito mana da Shugabanmu Annabi Muhammadu zuwa ga duniyar Halittu.

Mahaifiyarsa Aaminatu ta haifeshi acikin wannan dare mai girma. Kuma daga aure ya fito ba daga 'barna ba.

Don haka Alkhairi da Fifiko yazo tare dashi wanda ya gigita hankula da basirori. Kamar yadda Hadisai da Sahihan labarai suka tabbatar.

Mun gabatar da wannan karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp -(1) aranar 21-12-2015. {07064213990}.

ZAUREN FIQHU : Maraba da sauka Ya Shugaban Halittun Allah!!

Salati da amincin Allah su tabbata tare dakai adadin dawwama da wanzuwar tsarkin Mulkinsa.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI